Matsayin tsarin mulkin Najeriya dangane da barin jam′iyyar siyasa | Amsoshin takardunku | DW | 21.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Matsayin tsarin mulkin Najeriya dangane da barin jam'iyyar siyasa

Dokokin Najeriya sun bai wa 'yan majalisun dokoki ko kuma gwamnoni damar ficewa daga jam'iyyun da aka zabesu idan har suna fama da rigingimun cikin gida.

Tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ko dai 'yan majalisar dokoki ko kuma gwamnoni damar ficewa daga jam'iyyar da aka zabesu a karkashinta, muddin dai jam'iyyar tana fuskantar rigingimu ko kuma ta rushe.

Masana harkokin shari'a sun nunar da cewar inda za a fuskanci matsala shi ne idan jam'iyya na dunkule, babu rarrabuwar kawuna a cikinta.

Domin karin bayani, za ku iya sauraren shirin a kasa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin