Matsayin Jamus a kan rikicin Masar | Siyasa | DW | 09.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsayin Jamus a kan rikicin Masar

Ministan harkokin waje na tarayyar Jamus Guido Westerwelle, ya bayyana damuwansa dangane da mummunan tashin hankali da kasar Masar ta tsinci kanta a ciki.

A sakon da ya wallafa ta yanar gizo ta twitter, ya yi kira ga dukkan bangarorin da abun ya shafa da su guji jefa kasarsu cikin halin kaka-ni-ka-yi.

Westerwelle ya jaddada bukatar daukar matakai na gaggawa wajen samar wa Masar makoma a siyasance. Baya ga haka shafin ma'aikatar harkokin wajen na Jamus ya yi gargadi dangane da tafiye-tafiye zuwa yankunan da ba wuraren yawon shakatawa ba. Kazalika jami'ar kula da harkokin ketare ta Kungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton, ta fito fili ta jaddada bukatar daukar matakan shirya sabon zabe a kasar ta Masar.

Yawancin 'yan masar da ke zaune a nan Jamus dai kamar 'yan uwansu da ke can, na da sabanin ra'ayi dangane da siyasar kasar duk kuwa da cewar, akasarinsu na muradin ganin cewar an samu cimma zaman lafiya tare da ficewa daga wannan sabon rikici mafi muni tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaba Hosni Mubarak. Rashad dai dan Masar ne da ke zama a nan Jamus, wanda ke da ra'ayin cewar wadannan kalamai na diplomasiyya basu isa yin tasiri kan halin da ake ciki a kasarsa ba. A kan haka ne ya bukaci gwamnatin Jamus da ta basu goyon baya wajen tabbatar da demokaradiyya mai dorewa a Masar.

CAIRO, EGYPT - JULY 08: Pro Mohamed Morsi supporters rally near where over 50 were purported to have been killed by members of the Egyptian military and police in early morning clashes on July 8, 2013 in Cairo, Egypt. The military, which took over control of the country from Muslim Brotherhood leader Morsi last week, has denied that they opened fire on the protesters and claim the shootings resulted after they came under attack from members of the Muslim Brotherhood. Egypt continues to be in a state of political paralysis following the ousting of Morsi by the military. Adly Mansour, chief justice of the Supreme Constitutional Court, was sworn in as the interim head of state in a ceremony in Cairo on the morning of July 4. (Photo by Spencer Platt/Getty Images)

Masu gangamin goyon bayan Mursi

A birnin Berlin dai magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Mursi na ci gaba da gudanar da gangami, wadanda kuma suka lashi takobin ci gaba cikin makonni ko ma watanni masu zuwa, har sai sojojin sun tsame hannunsu daga harkokin siyasar Masar.

To sai dai akwai shakku dangane da ko bangarorin da ke rikicin zasu saurari wannan kira na diplomasiyya da kunnuwan basira. Ruprecht Polenz shine shugaban komitin kula da harkokin waje na majalisar dokokin Jamus.

Ya ce "a nawa tunanin, da ma sojoji basu saki ragamar mulkin kasar ba, ko bayan da aka kifar da gwamnatin Mubarak. Kasancewar dasu aka tsara matakan komar da kan kasar kan tafarkin demokradiyya da rubuta kundin tsarin mulkin, kasar zuwa zaben da ya bawa jam'iyyun masu kishin addini muslunci rinjaye, na su yi aiki kafada da kafada wajen tabbatar da matsayinsu a fannin tattali a gwamnati".

Dan majalisar tarayyar na jam'iyyar CDU ya yi tsokaci dangane da ci gaban ayyukan raya kasa da Jamus ke gudanarwa a kasar ta Masar, da suka hadar da inganta samar da ruwan sha mai kyau da inganta fannonin kiwon lafiya da ilimi.

epa03781647 (FILE) A file photo dated 17 July 2011, shows the then newly appointed Minister of Finance Hazem Beblawi during a press conference in Cairo, Egypt. According to an Egyptian presidency statement on 09 July 2013, Hazem Beblawi was named as Egypt_s new Prime Minister, while Mohamed Elbaradei was appointed Vice President for foreign relations. EPA/STRINGER +++(c) dpa - Bildfunk+++

Sabon Primiya Hazem Beblawi

Ya ce "wadannan abubuwa ne da ke da muhimmanci ga al'ummar Masar, saboda suna da tasiri ga rayuwarsu. A yanayin da ake ciki na rigingimu a yanzu haka, zai hana ci gaban gudanar da aikin, kuma ya zamanto dole da a tsayar da shi".

Kokarin kafa gwamnatin farar hula da sojojin Masar suke ikirarin yi dai, kawo yanzu ya ci tura. Jam'iyyar 'yan Salafiyyan Masar din dai, ta ki amincewa da nadin tsohon direktan hukumar kula da nukiliya ta duniya Mohammed Elberadei a matsayin Fraiminista. Kafofin yada labaran kasar dai sun sanar da nadinshi a matsayin mataimakin shugaban kasa, a yayin da aka nada Hazem Beblawi a matsayin fraiministan riko.

Mawallafiya: Zainab Mohammed abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin