Matsayin Amirka kan matakin soji a Siriya | Siyasa | DW | 30.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsayin Amirka kan matakin soji a Siriya

Amirka na tattauna yiwuwar ɗaukar matakin soji kan Siriya bayan da majalisar dokokin Birtaniya ta ƙi amincewa da ƙudurin ɗaukar matakin da David Cameron ya miƙa mata.

US President Barack Obama(L) and US Secretary of Defense Chuck Hagel stand for the American National Anthem during a ceremony to commemorate the 60th anniversary of the signing of the Armistice that ended the Korean War, at the Korean War Veterans Memorial in Washington, DC, July 27, 2013. AFP PHOTO / Saul LOEB (Photo credit should read SAUL LOEB/AFP/Getty Images)

Barack Obama da ministan tsaro Chuck Hagel

Bayan da aka yi zargin amfani da makamai masu guba a Siriya, rikicin ya yi ta ɗaukar hankali a duk kafafen yaɗa labaran duniya. Daga farko an zaci cewa ƙasashen Birtaniya, Amirka da Faransa za su ɗauki matakin soji a kan Siriya, to sai dai a halin da ake ciki yanzu, Birtaniya ba za ta kasance cikin waɗanda za su ɗauki matakin sojin da ake hasashen ɗauka ba, bayan da majalisar dokokin ƙasar ta kaɗa ƙuri'ar rashin amincewa da wannan mataki.

Bayan da Birtaniya ta janye, Amirka ma ta fara tattauna yin gaban kanta wajen ɗuakar matakin soji kan Siriya, Yanzu haka dai hukuncin da Obama zai yanke zai dangana ne kan abubuwan da zasu kawo haɗin kan ƙasashen a cewar mai magana da yawun kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya Caitlin Hayden, wadda ta yi baiyani bayan da majalisar dokokin Birtaniyar ta ƙi amincewa da matakin.

WASHINGTON, DC - AUGUST 26: U.S. Secretary of State John Kerry delivers a statement about the use of chemical weapons in Syria at the Department of State August 26, 2013 in Washington, DC. Kerry said that chemical weapons had been used to kill scores of people during the ongoing civil war in Syria and that the government of President Bashar al-Assad had used shelling to destroy the evidence. (Photo by Chip Somodevilla/Getty Images)

John Kerry sakataren kula da harkokin wajen Amirka

Yadda al'ummar Amirka ke kallon matakin Birtaniya

Gidan talabijin na CBS a Amirka ya rawaito wani mai riƙe da babban muƙamin gwamnati yana cewa "Bai kamata mu jira su ba, mu kanmu zamu iya yanke ta mu shawarar". Da yammacin jiya dai shugaba Barack Obama ya gana da manyan jami'an majalisar dokokin ƙasar ta wayar tarho inda ya bayyana musu matakin da yake so ya ɗauka kan Siriya.

Abin da ya fi mahimmanci shi ne gwamnatin Amirkan ta tabbatar cewa dakarun gwamnatin Bashar al-Assad ne suka yi amfani da makamai masu guba kan fararen hulan ƙasar. Kamar yadda ɗaya daga cikin waɗanda aka zanta da su ya bayyana daga baya. Haka nan kuma mai magana da yawun shugaba Obama Josh Earnest ya sake jaddada wannan batu

ARCHIV - Der Sohn des letzten syrischen Präsidenten Hafez al-Assad, Maher (l) und ein mutmaßlicher Erbe, Bascher, aufgenommen am 13.06.2000 in Damaskus (Syrien). Im Kampf gegen seine politischen Gegner verlässt sich der Clan von Syriens Präsident Assad auf den Geheimdienst und Einheiten der Armee, die sein Bruder Maher befehligt. Begleitet werden die Soldaten bei ihren Strafexpeditionen von einer furchterregenden Miliz des Regimes. Foto: Ramzi Haidar afp (Zu dpa 0499 «Gespenster der Armee treiben Syriens Armee an» vom 17.06.2011) +++(c) dpa - Bildfunk+++

Bashar al - Assad

"Mun san cewa gwamnatin ta yi amfani da makamai masu guba kan fararen hulan Siriya, mun kuma san cewa gwamnatin Assad ta mallaki ajiya na irin waɗannan makamai"

Hasashen 'yan gwamnatin Amirka

Ma'aikata a gwamnatin Amirkan na yaɗawa a kafofin yaɗa labarai cewa sun san shugaba Obama yana gab da yanke shawarar, tura dakaru zuwa Siriya na wani taƙaitaccen lokaci su kai hari, kuma a yanzu haka an tura jirgin ruwan yaƙi na biyar zuwa gaɓar ruwan Siriyar.

To sai dai duk da haka, 'yan majalisar dokokin Amirkan su ma suna so a ji ra'ayinsu na ko suna so a ɗauki matakin sojin koko a a. 200 daga cikinsu sun riga sun turawa Obama wasiƙar cewa kafin ya ɗauki matakin soji dole ya nemi ra'ayin majalisa. Inda suka ce duk da cewa dokokin ƙasar sun tanadi ɗaukar irin wannan matakin a yanayin da ke tattare da barazana, suna so ya sanar da su a hukumance kafin ya ci gaba a cewar shugaban kwamitin da ke kula da harkokin ƙasar waje a majalisar dattawan ƙasar Senata Meinandes

Britain's Prime Minister David Cameron is seen addressing the House of Commons in this still image taken from video in London August 29, 2013. Cameron said on Thursday it was unthinkable that Britain would launch military action against Syria to punish and deter it from chemical weapons use if there was strong opposition at the United Nations Security Council. REUTERS/UK Parliament via Reuters TV (Foto: Reuters) / Eingestellt von wa

David Cameron a Majalisar dokoki

Batutuwan da za su yi tasiri kan shawarar shugaba Obama

Bayan da ƙudurin ɗaukar matakin sojin Firaministan Birtaniya David Cameron ya sha ƙasa a majalisar dokokin ƙasar, zai yi wuya a ce shugaba Obama na Amirka ya kai nasa ƙudurin majalisa, bisa bayyanan da ke fitowa daga wasu majiyoyi masu tushe a gwamnatin na Obama, shawarar da zai yanke na la'akari ne da batutuwa guda biyu.

Na farko shi ne a hukunta Siriya kan batun haƙƙin ɗan adam, domin bisa tanadin dokokin ƙasa da ƙasa ta take haƙƙin bil adama, na biyu kuma shi ne ƙawayen Amirka kamar Israila da Turkiyya da ita ma Amirkan kanta, za su fuskanci barazana idan har makaman masu guba suka faɗa hannun ɓata gari.

Gidan Talabijin na CBS ya bayyana cewa a yau juma'a talatin ga watan Ogusta ne hukumomin leƙen asirin Amirka za su wallafa bayyanan da ke ɗauke da hujjojin cewa gwamnatin Assad ce ta yi amfani da makamai masu guba.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin