Matsayin Afirka Ta Kudu a rikicin Afirka Ta Tsakiya | Labarai | DW | 04.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsayin Afirka Ta Kudu a rikicin Afirka Ta Tsakiya

Afirka Ta Kudu ta ce za ta janye dakarunta daga jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya, bayan asarar sojojin da ta yi.

Shugaban kasar Afirka Ta Kudu Jacob Zuma ya sanar da cewar, kasarsa za ta janye daukacin dakarunta daga jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya, bayan dakarunta 13 sun mutu yayin fito na fito da 'yan tawayen da suka yi nasarar kifar da gwamnatin shugaba Farancoir Bozize. Shugaban ya dauki wannan matakin ne, bayan sukar da yake ta sha dangane da asarar dakarun da kasar ta yi, wanda ke zama mafi yawa - a lokaci guda, tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar ta Afirka Ta Kudu.

Idan za'a iya tunawa dai akalla dakaru 13 ne suka mutu, yayin da wasu 27 kuma suka sami rauni a ranar 23 ga watan Maris daya gabata, sa'ilin da 'yan tawayen Seleka da yawansu yakai mayaka dubu ukku suka isa kusa da Bangui, babban birnin jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya, inda daga baya kuma suka yi nasarar kifar da gwamnatin da ke mulki a kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal