Matsayin Afirka kan kisan na Ruwanda | Siyasa | DW | 10.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsayin Afirka kan kisan na Ruwanda

Masu lura da al'amura na ci gaba da dasa ayaar tambaya dangane da irin rawa da masana da 'yan siyasar Afirka suka yi kan kisan kare dangin na Ruwanda.

A wannan lokaci da ake ciki na tunawa da abubuwan da suka wakana shekaru ashirin da suka gabata kan batun kisan kiyashin da aka yi a Ruwanda, ya kasance wata dama ga bengarori da dama na tofa albarkacin bakunan su kan wannan lamari mai munin gaske, inda kama daga wadanda suka aikata wannan danyan aiki, da wadanda suka fuskanci kalubalen tare da rasa dangin su ga baki daya ta dalilin hakan, da ma manyan kasashen da ake ganin sun taka wata rawa cikin wannan lamari na kisan kiyashi,dukannin su sunyi bayannai tare da fatan nan gaba kar a taba samun irin abun da ya wakana a kasar ta Ruwanda.

Inda su ma daga nasu bangare masana na Afirka suka tofa albarkacin bakunan su a matsayin tuna baya da ma halin da ake ciki yazu dangane da iri-irin wannan batu.

Boubacar Boris Diop, wani marubuci ne dan kasar senegal, da ya tubuta littafi kan wannan batun na kisan kiyashin da aka yi a Rwanda.

"Kisan kiyashin da akayi a Rwanda ya kasance tamkar wani madubi ne, da ya kamata mu yan Afirka musamu kuzarin kallon kan mu cikin sa, dan mu gano laifukan mu, sannan kuma mu tambayi kanun mu cewa mi yasa nan da nan mu yan Afirka ake tofa mana miyau ga fuska."

Da ya ke magana kan batun zargin da ake yi wa masana da dama na Afirka da ma yan siyasa na rishin tashi tsaye kan batun kisan kiyashin da ya wakana a kasar Ruwanda, Farfesa Mamadou Samake, malami a Jami'ar birnin Bamaco ta kasar Mali, cewa ya yi:

"Ni a gani hakan ta faru ne dangane da yanayin da ake ciki a wancan lokaci, domin idan kuna tune iskar Demokradiya ta fara kadawa ne a wajejan shekara ta 1990, a wannan lokaci kungiyoyin fararan hulla na cikin shirye-shiryen kafuwa ne basu su dai zamna ba da gindin su, kuma mafi yawan ma'ilimantan sun rayu ne a kalkashin tsari na Jam'iya guda."

A cewar Marubuci Diop na kasar Senegale akasarin masana a wancan lokaci dama yan siyasa na Afirka, basu taka rawar da ta kamata ace sun taka ba, a matsayin su na yan Afirka yayin da wasu ma basu cikeken sani abun da ya faru inda shi kansa yace saidai yaje wannan kasa ce ya gane gaskiyar lamarin:

Idan ina tataunawa da kwararrun masana na Afirka wadanda ma suka shahara, suna kallon duniya ne da musalin kasashen turawa, ni kuma wani darasin da na koya kan batun kisan kiyashin da akayi a Ruwanda na yan Tutsi, sai kawai inga cewa kamar kayi kirari ne ka buga ma kanka yuka, domin babu zancan wannan Hutu ne ko wancan Tutsi ne tunda dukannin su harshe guda suke ji, adinan su guda, dan haka ni a ganina idan dan Hutu ya kashe dan Tutsi kamar yayi wa kanshi barna ne.Dan haka idan da tunani bai kamata ace Hutu sun yi abun da sukayi kan yan Tutsi ba.

Saidai daga nashi bengare Farfesa Mamadou Samake, malami a Jami'ar birnin Bamako na kasar Mali, na ganin cewa a wannan lokaci ana iya cewa yanayin masana na Afirka da ma tunanin su ya sha banban sosai ga yadda aka sani a shekarun baya, saidai kuma matsalar da wani lokaci yan siyasa ke haddasa wa:

"Al'ummomi na kasashe sun jima suna rayuwa tare ba tare da matsala ba, a nan abun da zance shine na a ja hankullan yan siyasar mu na Afirka, da su daina anfani da batun kabilu, ko na adinai c ikin lamarin su na siyasa."

A halin yanzu dai sabanin yadda aka fuskanta a wancan lokaci inda kafofin yada labarai suka taka rawar gani wajan hura wutar rikicin yanzu kuma ta yanhar su ce aka sake bi wajan aika sakonnin zaman lafiya tsakanin kabilu tare da yashefewa juna sabili da abun da ya faru ya riga ya faru.

Mawallafi: Salissou Boukari

Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin