Matsayin adawa a Masar kan shirin Zabe | Labarai | DW | 10.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsayin adawa a Masar kan shirin Zabe

Jam'iyar National Salvation Front da kuma kungiyar 'Yan Uwa Musulmi sun yi watsi da shirin shugaban rikon kwarya na kwaskware kundin tsarin mulki tare da shirya zabe cikin gaggawa.

default

Sameh Aschur, daya daga cikin shugabannin NSF

Babbar jam'iyar adawar kasar Masar ta sa kafa ta yi fatali da shirin shugaban rikon kwarya na kwaskware kundin tsarin mulki da kuma gudanar da sabbin zabukan kan nan da watanni shida masu zuwa. Jam'iyar National Salvation Front ta ce shugaban rikon kwarya Adli Mansour bai yi shawara da ita ba kafin ya dauki wanna mataki. Hakazalaika ta nemi da a yi wa dokar da ya sa hannu a kanta gyaran fuska.

Ita ma dai kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta hambararren shugaba Mohammed Mursi ta yi watsi da shirin, inda cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce Adli Mansour ba shi da hurumin kwaskware kundin tsarin kasar ta Masar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da magoya bayan Mursi ke lasar takobin ci-gaba da tayar da kayar baya har sai an sako Mohammed Mursi. Mutane 51 ne dai suka rasa rayukansu a lokacin da sojojin suka bude musu wuta a barikin da ake kyautata zaton cewa tsohon shugaban na tsare.

Shi dai shugaban rikon kwarya Adli Mansour ya nada tsohon ministan kudin kasar Hazem el-Beblawi a matsayin sabon firaministan wucin gadi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu