1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin shan Giya

Abba BashirAugust 22, 2006

Cututtukan da shan Giya ke haifarwa

https://p.dw.com/p/BvVJ
Wasu mashayan Giya
Wasu mashayan GiyaHoto: picture-alliance/ dpa/dpaweb

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Haruna Lawal Abdu, daga Jihar Taraban tarayyar Najeriya. Malamin ya ce, Don Allah ina so a tambayar min Likita, ko wadanne irin cututtuka shan giya ke haifarwa?

Bashir: To dangane da wannan tambaya ta Malam Haruna Lawal Abdu, daga nan Jamus, na tuntubi Dr. Sharif Yahaya Musa, Likita a Asibitin nasarawa dake Jihar kanon tarayyar Najeriya,inda na fara da tambayarsa, ko wadanne irin cututtuka ake samu sakamakon shan giya?

Dr. Sharif : Assalamu alaikum. Wato ita shan giya takan haifar da abubuwa da yawa ga mai shan ta, wanda yake wannan fili ba zai ishe mu, mu yi bayanin su ba. Amma muhimmai dai daga ciki zamu iya saninsu ta wuraren da ta ke tattabawa, wanda daga wannan abubuwan da take tattabwa, shi zai sa mu gane irin illar da ta ke haifarwa.Misali idan kamar ta taba Hanta, zata iya haifar da cutar da muke kira Hepatitis, da cutar shawara, inda zaka ga idanun Mutum sun yi rawaya kuma zai iya samun zazzabi, kuma idan abin yai tsanani zata iya haifar masa da Cirrhosis, wannan cirrhosis shine wato ita hantar ta Mutum zara rika motsewa haka.Idan kuma muka koma daga bangaren jini,zata iya haifar da raguwar jini a jikin Mutum. Raguwar jini kuma yana faruwa saboda wato abubuwan da suke aikin samar da wadannan halittun jinin na jiki sunyi kasa-kasa, kamar su bone-marrow kenan.Har ila yau mai shan giya zai iya samun kiba irin mai cutarwar nan, haka jikin sa zai girma da yawa. Zai iya samun abin da muke kira gyambon-ciki wato Ulcer kenan. Idan muka shiga cikin abin da ya shafi zuciya, to zuciyar sa zata rinka bugawa da-yawa-da-yawa wanda ake kira (Arrhythmia)kenan, sannan ga hawan jini. Har ila yau kuma ita kanta zuciyar zata iya kumbura ta kara girma . Sannan ida aka koma bangaren kwakwalwar sa, rike abu zai rinka yi masa wahala, kuma zai rinka yawan mantuwa,sannan kuma kodayaushe ya rinka samun tangadi, ba sai lallai ma yana cikin mayen giyar ba. Wadannan sune wadansu yan-kadan daga cikin cututtukan da zasu iya samun Mutum mai shan giya, wadanda za mu iya fada a dan wannan fili.

Bashir: To likita su wadannan cututtuka da ka lissafa, ta hanyar shan giya kawai ake kamuwa da su ko kuwa a’a, ana iya kamuwa da su ta wadansu hanyoyi daban?

Dr. Sharif : A, akan samu ta wasu hanyoyin ma daban, kamar misalin Ulcer, ai akwai hanyoyin da sukan haifar da Ulcer ga mutum. kamar misalin (cardiomyopathy) a cikin zuciya kenan, kamar hawan jini, kamar (Hepatitis) ciwon hanta kenan , za’a iya samun su ta wadansu wuraren, kamar (Anemia), duk yawanci za’a iya samun su ta wadan su wuraren ma . Amma dai ina tabbatar maka da cewa mai shan giya ma zai iya kamuwa da wadannan cututtukan.

Bashir : To likita zaka ga cewar su sinadaran yin giya din abubuwane da al’umma suke amfani da su yau da kullum wajen abinci , misali kamar su Gero, dawa, masara , Alkama da dai sauransu, to idan haka ne kenan ita giya wadda ake yi a masana’antu a sa a kwalaba ita ce kawai giya ko kuwa a’a duk abin da aka sarrafa da wadannan nau’o’i na kayan abinci matukar dai zai haifar da maye sunansa giya?

Dr. Sharif : A’a to ai su din wadanda kake magana, ai sai sun samu wani lokaci,yanayin su ya jirkita kenan shine za su iya haifar da maye, kuma a wannan yanayi dama shan su ai ba shi da amfani.

Bashir: Likita to akwai wata cuta da shan giya ne kawai ke haifar da ita, wato ba’a samunta ta wata haya sai dai giya kadai, baya ga wadanda giya na haifar dasu kuma wadansu hanyoyi ma na haifarda su?

Dr. Sharif: Kamar dai yadda na gaya maka a dai wadanda na lissafa babu wacce baza a iya samu ta,ta wata hanya ba. A bin da nake nufi za’a iya samun su ta wadansu wuraren ba sai giya kawai ba.

Bashir: Shin Likita zama tare da mai shan giya yana sa a kamu da wani nau’i na cuta da ya samu sakamakon shan giya?

Dr. Sharif: A’a in dai kana tare da shi shawarwari kawai zaka rinka bashi, amma ba zaka kamu da wata cuta ba wadda shi ya samu sakamakon shan giya.Wato Ba’a Daukar cutar da su suka samu?

Bashir: To Likita wace shawara ce da kai ga Al’umma kenan?

Dr. Sharif: Babbar shawara ita ce a rabu da ita,kaga shine kariya kenan daga kamuwa da wadannan cututtukan da muka lissafa, a rabu da ita gaba daya ita ce shawarar da zamu bayar.Idan kuma mutum wani nasa ya na sha, Allah ya kiyaye, to akwai shawarwari da akan bayar,idan kuma mutum ba zai iya bawa na kusa da shi shawara ba to akwai wadan da suka kware, akan same su a Asibitoci kuma wasu akan same su a gidajen ma, amma dai an fi samun su a Asibitoci kamar su Psycologist wadanda zasu je su zaunar da mutum su ba shi shawarwari, kuma ba abu ne na rana daya ba, tunda mai yiwuwa ya dade ya na yi abu ne da zai iya daukan lokaci ana jan hankalin sa a hankali a hankali har Allah ya taimaka a samu nasara.

Bashir: Likita, ko da dai ba ni da hujja a ilimance, Mutane na cewa wai barin shan giyar ma idan dai mutum ya saba da ita yana haifar da cuta, wannan zancen gaskiya ne?

Dr. Sharif: E, gaskiyane, to amma ba zai hana ace don zai haifar da wani abu a daina shan ta ba, no, yana haifar da wasu abubuwa amma akan kai mutum asibiti idan sakamakon daina shan ya haifar da wadannan abubuwan. To kamar yadda na fada tun farko daina shanta shine muhimmi, kuma ni ma na ce a daina shanta. To sabodahaka idan aka ce mutum ya daina shanta ta haifar masa da wasu abubuwa, sai a garzaya da shi asibiti mafi kusa in Allah ya yarda akwai abubuwan da za’ai masa kuma zai rabu da abin da ya same shi, in-sha-Allah.