Matsalolin ilimi a Najeriya | Siyasa | DW | 09.11.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalolin ilimi a Najeriya

Masu ruwa da tsaki game da harkokin ilimi daga jihohin Najeriya sun shirya taro a kaduna domin laluben hanyoyin inganta karatu a ƙasar.

A yanzu haka dai ana ci-gaba da gudanar da taran ƙoli na malaman Nijeriya na kwanaki ukku dan nemo hanyoyin warware matsalolin dake addabar ilmi a makarantun firimari da sekandari da jami'o'in dake a fadin ƙasar.

A wannan Taro dai na tsawon kwanaki ukku mai taken bunƙasa ilmin malamai tare da koyarwasu dan magance taɓarɓarewar ilmi dake addabar 'yan Nijeriya,ya sami halartan manyan malamai daga Nijeriya da ƙasashen ƙetare da masu ruwa da tsaki da ƙwararrun masana a ɓangeren ilmin yara.

Burin gwamnatocin jihohin da na tarayyar Nijeriya shine na tabbatar da kawar da jahilci a cikin al'ummanta kamin nan da shekara ta 2015, dan cimma burin muradun ƙarni.

Farfesa Abubakar Garba Sulaiman na daga cikin waɗanda suka shirya wannan taro.Yace: mun gayyato masana daga kowane ɓangaren ilmi dan lalubu matsalolin dake sanya ɗallibai na faɗuwar jarabawa a Najeriya,ya ce muna san tabbatar da ganin cewa mun tattauna tare da ɗaukar ƙwararen matakai dan shawo kan bakin zaren wannan matsala.

Taɓarɓarewar ɓangaren ilmi a tarayyar Najeriya ta daɗe ta na haifar da illoli da janyo nakasu ga harkokin ci-gaban ƙasa musamman ma dai yankin arewa,a sabili da yadda darajar ilmin ke ci-gaba da zubewa ƙasa warwas.

A kwana na biyu da ake shiga wajan taran, ƙwararrun masana sun nuna takaicinsu, dangane da matsalolin ilmi daban-daban da suka tattaro suna ciwa hukumomi da malamai tuwo a ƙwarya,al'amarin da ke ƙara nunar da cewa malamai da yawar gaske a Najeriya sun fara yin bankwana da harkan koyarwa sakamakon tsananin talauci da rashin biyan su alabashi bakan lokaci,da kuma wulaƙancin da malaman ke fuskanta daga iyayen yara.

Fasfesa Abubakar Garba ya ci gaba da bayyana rashin jin daɗin sa kan yadda manyan Najeriya ke kwashe 'ya'yansu daga ƙasar suna fitar da su ƙasashen ƙetare neman ilmi.

Ya ce lokaci yayai da dukkanin shuwagabannin Najeriya dake kwashe 'ya'yan su suna zuwa karatu ƙasashen ƙetare da su daina,su dawo mu tattaru wuri ɗaya dan gyara darajar ilmin yaranmu.

Students of the African Institute of Mathematical Sciences. A school engineered towards getting the Next Einsteins from Africa. Foto: AIMS ( African Institute of Mathematical Sciences ) Cape Town, South Africa, Undatierte Aufnahme, Eingestellt 12.09.2011

Daya ke maida jawabi a wajan taran, ministan ƙasa a ma'aikatar ilmi Yesin Wiki cewa yayi gwamnatin tarayyar Najeriya ta jaddada ƙudurinta na bunƙasa sha'anin koyarwa a Najeriya, dan samar da ƙwararrun malamai,bugu da ƙari Yesin nunar da cewa gwamnatin Najeriya za ta samar da wani shiri da nufin samar da tsare-tsare dan bunƙasa harkan koyarwa a ko ina a cikin ƙasa.

Wasu 'yan Najeriya sun tofa albarkacin bakin su kamar hak:yaranmu basa iya karatu,dan saboda haka ne muke buƙatar hukumomi da su dawo da makarantun horar da malamai a cikin ƙasar,da kuma maido da karatun firamari na aji bakwai.

Duk da cewa a yanzu haka dai kashi 75 % na makarantun jihohin arewa masu zaman kansu na jama'ar kudancin Najeriya ne,kuma akwai baragurbin malamai da yawar gaske dake a makarantun gwamnati suna koyarwa,wannan ya sanya gwamnatin jahar kaduna ta fara yin waje da dukkanin malaman da basu cancanta su koyar a cikin makarantunta dan ya zamo wani mataki na farko na tsaftace harkan koyarwa a dukkanin makarantunta.

Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin

 • Kwanan wata 09.11.2012
 • Mawallafi Nigeria Bildung
 • Muhimman kalmomi Bildung
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16gKy
 • Kwanan wata 09.11.2012
 • Mawallafi Nigeria Bildung
 • Muhimman kalmomi Bildung
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16gKy