Matsaloli kalilan a zaben kasar Afirka ta Kudu | Siyasa | DW | 07.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsaloli kalilan a zaben kasar Afirka ta Kudu

Dubban 'yan Afirka ta Kudu sun yi dafifi a runfunan zabe domin kada kuri'unsu. Sai dai baya ga fara zabe da lati a Kalilan daga cikin runfunan zabe, tanshi hankula ya barke a daya daga cikin mazabun kasar.

A lokacin da aka fara kada kuri'a da misalin karfe bakwai da rabi agogon Afirka ta Kudu, mutane 20 ne ke shirye a layi na daya daga cikin runfunan zaben da ke makarantar firamare ta Hitekani da ke Soweto. Mampy Maluleke da ke da shekaru 60 da haihuwa na daya daga cikin wadanda suka dako asubanci domin ganin cewa sun sauke nauyin da ya rata musu a wuya.

Yayin da shi kuwa Phumelina Khoza mai shekaru 23 da haihuwa, ya na ganin cewa zaben wata dama ce a gareshi na zabar wa kasarsa wata kyakkyawar makoma. Ya na daya daga cikin 'yan Afirka ta Kudu da ke ganin cewa "ANC ta gaza a kan matsalar filaye, saboda ta yi alkawarin mayar wa 'yan asalin kasa kashi 30 % na filayen a cikin shekaru 20 na mulki. Amma ya zuwa yanzu kashi bakwai daga cikin 100 na fiyalen ne kawai aka mayar wa bakaken fata."

Wahlen in Südafrika

'yan Afirka ta Kudu sun yi dafifi a rufunan zabe

Wasu masu zabe sun juya wa ANC baya

Tuni ma dai wasu daga cikin 'yan Afirka ta Kudu suka bayyana jam'iyyar da suka kada wa kuri'arsu. Cheryl Mageza mai shekaru 29 da haihuwa ga misali, ba ta boye cewa ta juya wa ANC da ke mulki baya ba, saboda ta na ganin cewa ba abin da jam'iyyar ta tsinana a baya.

"Na dangwala wa Democratic Alliance. Na yi hakan ne domin nemar wa sa'o'ina da kuma wadanda suke da shekarun dana makoma ta gari. "

Duk dai da suka da gwamnatin Afirka ta Kusu da ke ci a yanzu ta ke ta sha, amma kuma bai hana mataimakin shugaban jam'iyyar ANC da ke mulki Cyril Ramaphosa yin alkawarin daidaita alma'ura idan Jacob Zuma ya danka masa harkokin mulki ba. Ya ce "Ni dai ban kadu ba saboda na yarda da da al'ummarmu. Jama'armu sun san wanda zai iya ciyar da wannan kasa gaba. Ina jin cewa nasara na tafe."

Cyril Ramaphosa Südafrika Wahlen

Cyril Ramaphosa na ANC ma ya kada kari'a

Rikici a daya daga cikin mazabu

Sai dai kuma an samu rahotannin tashe-tashen hankali tun gabanin zabe, inda masu zanga-zanga suka kona tantuna biyu na zabe a mazabar Bekersdal. Sai dai kuma komai ya daidaita daga bisani. A ranar asabar za a fara samun kwarya-kwaryar sakamakon zaben da ake jin cewa jam'iyyar ANC za ta lasheshi. Sai dai Kuma Jam'iyyun AD da kuma EFF sun ce za su bai wa marada kunya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin