Matsalar tsaro a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
November 26, 2013Kasar Faransa ta bayyana cewar, za ta aike da dakaru dubu daya zuwa Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya, a karkashin rundunar da Majalisar Dinkin Duniya za ta tura domin samar da zaman lafiya a kasar, wadda ke ci gaba da fuskantar rigingimu.
Ministan tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian, shi ne ya sanar da hakan, yini daya kachal bayan da wani babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya yi kashedi game da yuwuwar kissan kiyashi, da kuma barkewar yakin basasa a kasar, wadda ke zama daya daga cikin kasashen da suka fi fama da talauci a duniya, wadda kuma ke ci gaba da fama da rigingimu, tun bayan da 'yan tawayen kasar suka kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar, Farancoir Bozize a watan Maris.
Kungiyoyin kare hakkin jama'a dai na zargin 'yan tawayen da laifukan da suka hada da kissan jama'a, da yi wa mata fyade, da kuma tilastawa kananan yara shiga cikin aikin soji. Dama dai kasar Faransa tana da dakarun da yawansu yakai 420 a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya, galibinsu kuma, na bada kariya ne ga filin sauka da tashin jiragen sama na Bangui, babban birnin kasar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman