Matsalar Samsung Galaxy Note 7 | Zamantakewa | DW | 12.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matsalar Samsung Galaxy Note 7

Kamfanin kera wayar salula ta Samsung da ke kasar koriya ta kudu ya amince da tangardar da aka samu a manhajar wayar hannu da ya kera a baya-bayannan inda wayar ke iya fashewa yayin da ake cajinta

Abu na farko da kamfanin na Koriya ta Kudu ya yi shi ne na canzawa abokanan cinikayyarsa, wadanda suka riga suka sayi wayar, kafin ya umarci dukkanin sauran rasansa da ke a cikin sauran kasashen da su daina sayar da wayar ta Galaxy Note 7. Alexander Hirschle, Shi ne daraktan zuba jari a cibiyar kasuwanci ta Jamus da ke a Koriya ta Kudu.

Ya ce ''Yan Koriyan  sanannu ne a wannan fanni, don haka tun lokacin da suka gano matsalar da gaggawa suka shiga yin aiki domin kawo gyara ga matsalar"

 Samfurirn wayar hannu ta Galaxy Note 7 waya ce da ke da kima da daraja a kasuwani, ta fannin gogayaya da sauran samfurin waya na Smartphone ta Apple, amma tun lokacin da wannan al'amari ya faru darajar hannun jarin kamfanin na Samsung ta fadi yayin da kuma aka samu koma baya na masu saka jarin, a irin ja da bayan da kamfanin bai taba gani ba tun a shekara ta 2015.
Kana kuma wasu sauran kamfanonin masu kera wayar, wadanda yake a gabansu ko kuma suke yin goggaya irin su Apple da Lenovo da Huawei na China, wadanda su farashinsu ma yake kasa da na Galaxy, bisa ga dukkan alamu za su iya shiga gaban kamfanin na Samsumg .


A watan da ya gabata ne dai aka tilasta wa kamfanin kera wayoyin na Koriya ta Kudu da ya janye addadin wayoyin samfurin Galaxy Note 7  miliyon biyu da rabi, daga kasuwannin duniya, wannan mataki ya biyo bayan da aka samu wayoyin da rashin ingancin batura da ke haddasa hayaki lokacin cajinta, wanda hakan ya sa kamfanonin jiragen sama da dama suka haramtawa fasinjoji da ke da irin wayoyin shiga jiragensu .

Kamfanin na samsung a cikin shekaru gommai ya zama kamfanin latironik mafi girma a duniya. A shekara ta 2008 aka tilasta wa Lee Kun-hee, dan mutumin da ya kirkiro kamfanin da ke zaman jagoran yin marabus, saboda tabargazar da ya yi ta kudi. Kuma tun daga wannan lokacin bayan ficewarsa, sassan kamfanonin daban-daban suka hadu domin yin jagoranci. A yanzu haka kamfanin yana kerawa kana kuma yana sayar da jiragen ruwa da sorayen benaye, da talabijin, da wayoyin Smartphones, da magunguna da kuma kayan sanyawa.

Sama da kamfanonin guda 80 ke aiki, rassa daban-daban a karkashin kamfanin na Samsung, mai yawan ma'aikta dubu 500 wanda kuma yake da jari na sama da biliyan 300 tun daga shekara ta 2014.


Alexander Hirschle ya nuna mahimmancin kamfanin na Samsung a cikin tattalin arzikin Koriya ta Kudu, inda ya ce ''Kudaden ciniki da kamfanin yake samu ya kai kusan kashi 20 cikin dari na kudaden shiga na kasar ta Koriya ta Kudu, ba mamaki kamfanin ya dauki kwakkwaran matakai, domin farfado da koma bayan tattalin arzikin da ya kan iya fuskanta.''

A farkon shekara ta 1970  lokacin da kasar Koriya ta Kudu ke neman bunkasa hanyoyin tattalin arzikinta, ta rika tallafa wa man'yan kamfanonin kasar na latironik irinsu Samsung, da LG da Hyundai, ta hanyar ba su wata dama ta samun saukin kasuwancin domin bunkasa harkokinsu