1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar magungunan jabu a Ghana

February 27, 2013

Rahotani daga hukumar kiyon lafiya ta WHO ko kuma OMS,sun bayana cewar kusan kashi 64 daga cikin dari na maganin dake shigowa Afrika na jabu ne

https://p.dw.com/p/17n1a
Magungunan jabu sai karuwa suke yiHoto: DPA

Alkaluman hukumar majalisar dinkin duniya ta kiyon lafiya wato WHOko kuma OMS ,sun yi amanin cewar yaduwar kwayoyin magunguna na jabu dake shigowa a kasashe masu tasowa,na daya daga cikin abunda ke kara jiyo wasu sabbin cututuka ga jama'a,inda hasali ma ake sayarda su barkatai ba tare da mutane sun kiyaye da daukar matakai ba. Kodayake halin kuncin rayuwa musamman talauci na daya daga cikin abunda ke sa mutane na maida hankali ga magunguna ciki ma har da na gargajiya.

Kasar Ghana ma bata tsira ba ga wannan lamarin:Thomas Amedzro wani jami'i ne dake kulla da sa ido ga kwayoyin magani da ma abinci a karkashin wata hukuma ta kasar Ghana.

" Yace, matsalar magunguna na jabau har ta kai ga magunguna na gargajiya wato magani irin na itatuwa,kuma da dama daga cikin su suma na jabu ne"

Nahiyar Afrika dai ta kasance wani dandali ko kuma fili na zubar da shara ta magungunan irin na jabu na kowace kama a duniya. A shekara ta 2011,hukumar kiyon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya wato WHO ko kuma OMS,ta bayana cewar kusan kashi 64 daga cikin dari na adadin magungunan cutar maleria da tarayyar Najeriya tayi oda daga waje,sun kasance na habu ne,sannan a kasashen Uganda da Tanzaniya,can ma kusan makamancin wannan adadin na kwayoyin da aka shigo da su duk na iska ne.
Duk kwa da matakan da hukumomi a kasar Ghana ke dauka na yaki da kwayoyin jabu,matsalar sai dada karuwa take yi inji Thomas Amedzro jami'in kula da maganin jabu a kasar ta Ghana.

" Yace, a kasuwani,da tashoshin motaci,kai har da a wasu shagunan da ba ma kemes ne ba,za kaga mutane na saida magani kai tsaye kamar alawa,kaji irin yadda matsalar ke faruwa."

Kodayake jami'in ya kara da cewar galibin magungunan dake shigowa a kasar ta Ghana,da ma Afrika,na fitowa ne daga kasashe irinsu China,India,Pakistan ko kuma Indoneziya.
Shi ma James Lartey,wani abokin aikin Thomas ne dake cikin hukumar yaki da kwayoyin jabu,ya bada haske a kan irin barazanar kamuwar da miyagun cututka a dangane da amfani da wannan magungunan.

" Yace,idan mutun ya samu takardar sayen magani,sanna wai don wasu dalillai,yaje ya kabrawa kansa maganin jabu,ba wai zai samu saukin rashin lafiyar ne ba,illa dai cutar ta dada hau hauwa,kana idan mutun bai kiyaye ba to ba shakka,matsalar kan iya kaishi mahalaka."

Derrick Ekow Sam,wani ne da ya shaida irin bakar rashin lafiyar da ya sha sakamakon amfani da irin wannan maganin,yace shi ganau yake ba jiyau ba.

"Yace,na kamu da cutar maleria,da nije asibiti,aka hada nio da wani magani ashe irin na jabu ne,ai rashin lafiyar sai taki sauka,kaidai kada in kaiku nesa na share sama da makoni biyu gida kwance ko mtsawa ban iya yi. Da ni ji dan sauki ni rarafa can pharmacin da suka bani maganin,wai wani abu basu san na jabu ne ba."

A wasu kasashen dai,irinnsu Kenya da ma kudancin India,an samu dan ci-gaba kalilan tare da hadin gwiwar gwamnati inda ake baiwa masu kemes horo don gano makamantan ire iren wandanan magungunan.

Mawallafa: Carl Ofori/ Issoufou Mamane
Edita: Saleh Umar Saleh