1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar mace-macen mata a Afirka ta Kudu

October 9, 2014

Kungiyar kare hakin dan Adam ta Amnesty International, ta yi tsokaci kan yadda ake samun yawaitar mace-macen mata wajen haihuwa a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/1DSc5
TBC Tuberkulose Frau Patientin Südafrika
Hoto: Alexander Joe/AFP/Getty Images

A wani rahoto da ta fitar a wannan Alhamis, kungiyar ta ce fiye da kashi daya daga ciki uku na mutuwar mata da ake samu masu juna biyu a kasar ta Afirka ta Kudu, na da nasaba ne da cutar Sida, kuma abu ne da ake iya kauce masa.

Hukumomin wannan kasa dai, sun dauki matakai na samar da magungunnan rage kaifin cutar ta Sida ga mata, da ma 'yan mata masu juna biyu, tare da yi musu awon ciki kyauta. Sai dai duk da haka a cewar kungiyar ta Amnesty International matan kasar ba sa kula da zuwa asibitoci domin awon ciki. Kimanin mutane milian shidda ke dauke da kwayar cutar Sida a kasar ta Afirka ta Kudu, kwatankwacin fiye da mutum daya cikin goma ne ke dauke da wannan cuta a kasar ta Afirka ta Kudu.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu