Matsalar fyade a jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo | Labarai | DW | 26.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar fyade a jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo

Birtaniya ta yi alkawarin tallafawa wadanda matsalar fyade ta shafa a Kongo

Sakataren kula da harkokin wajen Birtaniya William Hague ya bayyana cewar kasarsa sa za ta samar da kudaden da za'a yi anfani da shi wajen tattaro bayanan da suka shafi wadanda 'yan tawaye suka yi musu fyade a lokacin tashe tashen hankulan da jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo ta fuskanta. Sakataren harkokin wajen na Birtaniya, wanda ya kai ziyarar aiki zuwa Kongo, tare da rakiyar wata fitacciyar 'yar wasan Film nan a kasar Amirka Angelina Jolie, domin nuna damuwa game da matsalar yin anfani da fyade a matsayin makami a lokacin yaki, ba su sami zuwa asibitin Bukavu da ke yankin gabashin Kongon ba, saboda rashin kyawun yanayi. A dai asibitin ne malaman jiyya ke kula da wadanda matsalar fyaden ta addaba. Ofishin kula da harkokin ketare na Birtaniya ya ce dama an shirya sakataren, zai gana tare da likitocin kungiyar kare hakkin jama'a, wadanda ke tallafawa marasa lafiyar. Hague ya bayyana kudirin bayar da gudummowar kudin daya kai Euro dubu 205 domin tattara bayanan.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal