Matsalar fasa kwaurin hauren giwa a Togo | Labarai | DW | 29.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar fasa kwaurin hauren giwa a Togo

Mahukunta a Lome sun yi babban kamu mafi girma kan kisan giwaye da ake yi ba bisa ƙa'ida ba, abinda duniya ta haramta bisa dokokin ƙasa da ƙasa

'Yan sanda a ƙasar Togo sun kama mutane uku da aka zarga da yin safarar kimanin ton biyu na hauren giwa. Jami'an gwamnati suka ce an samu kayanne cikin buhunna a wata kwantaina da aka shirya turawa zuwa ƙasar Vietnam. Kayan da aka kama ya nuna an kashe giwaye 230, wanda shine kamun hauren giwa mafi girma da aka taɓa samu a yakin ƙasashen yammacin Afirka. A 'yan shekarunnan dai, ƙasar Togo ta ƙaddamar da yaƙi da masu fasa ƙwaurin hauren giwa, lamarin ƙasar ta yi suna a kai tun shekaru.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu