Matan Ghana da irin basirarsu
Don raya bikin ranar mata ta duniya, tashar DW ta wallafa hotunan matan kasar Ghana, bisa kokarin da suke na gudanar da ayyuka na iya dogaro da kai da kuma daukar dawainiyar iyali tare da samar da ci-gaban al'umma.
Lokacin shuka
Lokacin shuka na da matukar mahimmanci ga mazauna karkara. Da zarar ruwan sama ya sauka, mata na mayar da hankali don cika burin samun albarkatun noma. Duk da karancin taimakon da suke samu daga mazajensu, a lokuta da dama matan na gudanar da ayyukansu ne da taimakon 'yan uwansu.
Arziki a sana'ar tuki
Duk da cewa ba kasafai aka san mata da wannan sana'a ba, mata a Ghana sun tunkari wannan jan aiki, inda suka tsunduma cikin sana'ar tukin motar fasinja. Yanzu ba sabon abu bane ganin mata na tuka manyan motoci a kasar. A sassan duniya an shaida cewa mata sun fi yin taka tsantsan wajen tukin mota fiye da takwarorinsu maza.
Aikin tsaro
'Yan sanda na fareti a garin Tamale, inda mata ke sahun gaba domin nuna irin bajintarsu kan sha'anin tsaro da kuma irin taimakon da suka shirya bayarwa a fannin samar da zaman lafiya a sassan kasa. A kwanakin baya-bayan nan ne mata suka sami damar shiga aikin 'yan sanda.
Nemo itacen girki
Sakamakon karancin makamashi na yin girki, matan karkara a Ghana na tafiya mai nisa domin yin itace kafin su dafa abincin da iyalinsu za su ci. Wannan kuwa ya kara haddasa mummunar dabi'ar nan ta yawaita saran itace don amfanin girki.
Aikin shikar 'ya'yan kadanya
Bayan samun albarkatun noma, mata na mayar da hankali wajen sheke 'ya'yan kadanyar da ake gasawa kafin samun man da ake anfani da shi domin iyali ko sayarwa.
Dabarun busar da kadanya
Mataki na biyu shi ne yadda za a busar da 'ya'yan kadanyar kafin a sarrafa zuwa mai. Matan na yin hakan ne ta hanyar zama cikin shiri domin gujewa saukar ruwan sama.
Matakin yin gashi
Gashin 'ya'yan kadanyar, mataki ne na fidda mai don amfanin al'umma, kuma wannan aiki ne da mata a arewacin kasar Ghana suka kware a kai, akasarinsu na yin aikin don samun abun ciyar da iyali.
Albarkatun noma
Bayan daukewar damina, doya na daga cikin albarkatun noma da ake fara girbewa. A dalilin hakan ake gudanar da kasaitaccen biki domin nuna farin ciki na yalwar da aka samu. Iyali za su sami wadatar doyar har su kai saura kasuwa su sayar ga al'umma.