1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matan Afirka na nuna bajinta a harkar fina-finai

Usman Shehu Usman
March 3, 2017

Masu hada fina-finai sun halarci bikin nuna banjinta na FESPACO a Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso. Abin da ya fi daukar hankali a wannan karo na 25 shi ne irin rawar da mata ke takawa a fagen shirya fina-finai a kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/2YanY

A yayin nuna fina-finan na FESPACO akwai abubuwan ban sha'awa da yawa, musamman fim wasu matan hudu da suka yi tattaki daga Dakar na kasar Senegal har i zuwa Eko a Najeriya, . Daya daga cikin matan ita ce Emma 'yar kasar Côte d' Ivoire, wacce ta yi ta simogal zannuwa don samun kudin da zata biya karatun 'ya'yanta. 

Naky Sy Savane wata mawakiya a Côte d' Ivoire na cikin wadanda fiilm din matan ya burge, kuma ta yi farincikin ganin "a karon farko a bude bikin fina-finan da fim din mata. Wannan fice ne ga dukkan matan Afirka, wadanda ko da yaushe ake barinsu a baya."
Kusan dai duk fina-finan na bana na bayyanan irin matsalolin da matan Afirka ke fuskanta a rayuwa. Wasu daga cikin matan da suka taka rawa sun hada da Aisha wata 'yar kasar Tanzaniya: Sai kuma Fatou Toure Ndiaye 'yar kasar Senegal, wacce ta hada fimta kan wata 'yarinya da aka yi wa kishiya.

Afrikanischer Film Burkina Faso Naky Sy Savané
Naky Sy Savane na hada fina-finai a Côte d' IvoireHoto: DW/K.Gänsler

Ta ce ta zabi "wannan labarin domin ni kaina Musulma ce. Zama da kishiya a cikin jama'armu kusan ko wane gida ana samunsa."

Batun 'yan gudun hijira da ke tsallakawa daga Afirka i zuwa Turai ma ya samu shiga, inda aka hada fim kan yadda kasashe da ke da iyaka da tekun Bahrum ke fuskantar kwararar baki. Naky Sy Savane ta ce "Wadannan matan ne ginshikin sajewar bakin da ke shigowa."

Bikin nuna fina-finan wanda aka fi sani da FESPACO, an fara gudanar da shi ne tun a shekarar 1969.  An dai dauki tsauraran matakan tsaro a kewayen inda bikin ya gudana, kasancewar Burkina Faso ta fuskanci harin 'yan ta'adda a shekarun baya-bayannan.