1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaNa duniya

Cutar AIDS zama annoba a duniya

Suleiman Babayo MA
March 24, 2025

Cutar AIDS tana iya zama annoba ga duniya baki daya sakamakon matakin Amurka na katse taimakon agajin kasashen duniya, kuma tilas a maye gurbin taimakon idan ana neman kare duniya daga shiga annobar cutar ta AIDS.

https://p.dw.com/p/4sC1v
USAID
USAIDHoto: MANDEL NGAN/AFP via Getty Images

A wannan Litinin hukumar lkula da cutar AIDS ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa za a samu sabbin masu kamuwa da cutar 2,000 a kowace rana a duniya sakamakon matakin Amurka na katse taimakon da take yi na yaki da cutar.

Karin Bayani: Najeriya za ta dauki nauyin ma'aikatan USAID

Hukumar ta ce muddun Amurka ba ta dawo da tallin dakile cutar ba, kuma ba a samu maye gurbin taimakon na Amurka ba, nan da shekaru hudu za a samu kimanin mutane milyan 6.3 sabbin masu kamuwa da cutar ta AIDS ko SIDA, gami da samun karin masu mutuwa daga cutar. Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce haka zai janyo cutar ta AIDS ta zama annoba tsakanin kasashen duniya.