Nada gwamnatin yankin Tigray
March 23, 2023Talla
A wannan Alhamis gwamnatin Habasha ta nada babban jami'i a kungiyar TPLF a matsayin wanda zai jagoranci yankin Tigray sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya da ta kawo karshen rikici tsakanin bangarorin biyu na tsawon shekaru biyu.
Firaminista Abiy Ahmed na kasar ta Habasha ya bayyana nada Getachew Reda a matsayin shugaban yankin Tigray na wucin gadi, kamar yadda sanarwa daga fadar firaministan ta tabbatar.
Wannan sanarwa ta zo kwana guda bayan majalisar dokokin kasar ta Habasha ta cire sunan jami'an TPLF daga cikin jerin 'yan ta'adda da aka saka lokacin rikicin kasar.