Matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin Birtaniya | Labarai | DW | 22.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin Birtaniya

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana matakan tsimi da tanadi domin riga kafi ga abkuwar kariyar tattalin arziki

default

Jawabin ministan kuɗin Birtaniya gaban Majalisa

A yunƙurin riga kafin ga faɗawa cikin matsalar tattalin arziki, ministan kuɗin Britaniya ya bayyana matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.A jawabin da ya yi gaban Majalisar Dokoki wajen gabatar da wannan shiri ministan kuɗin Britaniya George Osborne cewa ya yi:

"Wannan kasafin kuɗi na da mahimmanci ta la´akari da yadda zai cike giɓin  kuɗaɗen da mu ka yi asara baya , ya kuma yi riga kafinn faɗawa cikin matsalar tattalin arziki.Ya zama cilas mu ɗauki wannan mataki, abinda ya tura kusu wuta ne ya fi wuta zafi, saboda mun yi gadon bashi mai tarin yawa daga gwamatin da ta shuɗe."

Daga jerin matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin, Britaniya ta ƙara yawan haraji daga centi 17 zuwa 20.

A jawabin da ya yi gaban Majalisa Osborne ya bayyana goyan baya ga Fransa da Jamus wajen ɗaukar matakin bai ɗaya, na ɗorawa bakuna sabin haraji a matsayin hanyar cika giɓin tattalin arziki.Ƙasashen ukku sun ce za su tattana wannan batu tare da sauran membobi ƙungiyar G20 da ta ƙunshi ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na duniya a zaman taron da zasu shirya ƙarshen wannan mako a Kanada.

Tuni shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban ƙasar Faransa Nikolas Sarkozy sun rubuta wasiƙar haɗin gwiwa zuwa ga Firaministan Kanada Stephen Harper inda suka buƙaci ya bada haɗin kai, domin yaɗa wannan manufofi a sauran ƙasashen ƙungiyar G20.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Ahmed Tijani Lawal