Matakan tsaro a lokutan Sallah a Najeriya | Siyasa | DW | 14.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matakan tsaro a lokutan Sallah a Najeriya

A kokarin ganin an yi bikin babbar Sallah cikin kwanciyar hankali da lumana hukumomin tsaro a Najetiya musamman a jihar Filato sun tattauna da shugabannin addini.

Jami'an tsaro a jihar Filato sun gudanar taro na hadin guiwa da shugabannin addinai, tare da na matasa don ganin an yi hidimar babbar Sallah cikin lumana da kwanciyar hankali a jihar.

Makasudin wannan ganawa dai shi ne don kara janyo hankulan jama'a, da zummar cimma zaman lafiya a jihar a lokacin bukukuwar babbar Sallah, kasancewar an fuskanci tashin-tashina a shekarun baya a lokaci kamar haka.

Shirin ko ta-kwana a Jos da kewaye

Shugabannin addinin Musulunci da na Kirista ne tare da matasa daga bangarorin addinan biyu suka hallara inda kwamshinan 'yan sandan jihar Filato Chris Alakpe, ya fayyace cewar ko da shi ke yanzu an cimma zaman lafiya musamman ma a birnin Jos da kewaye, duk da hakan jami'an tsaro za su kasance cikin shirin ko ta-kwana don kawar da duk wata barazana ta tsaro a lokacin hidimar Sallah da kuma bayan Sallar.

Rev. Joseph Bot, shi ne daraktan kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista ta (PPMI), ya yi karin haske kan abin da aka tauttauna a taron inda ya ce.

"Taron ya duba batun tsaro ne a lokacin hidimar Sallah kana ya duba irin gudummawar da kowa zai bada wajen samun zaman lumana a jihar a lokacin bukukuwan babbar Sallah."

Bin umarni da ka'idoji shi ne mafi a'ala

Jami'an tsaron na Filato dai sun nemi ganin al'umma sun bi umurni da ka'idojin da aka gindaya a baya dangane da yadda za a gudanar da shagulgular babbar Sallah a bana.

Malam Sani Suleman shi ne shugaban kungiyar matasan Musulmi na jihar Filato, ya ce ganawar da ake yi tsakanin jami'an tsaro da shugabanin al'umma a lokacin bukukuwa kamar haka yana da matukar fa'ida.

"Tattaunawa tana da fa'ida sakamakon cewar a irin wannan ganawa ce ake kara samun fahimta tsakanin mabiya addinan biyu."

To sai dai kuma domin kyautata yanayi na tsaro, a 'yan shekarun baya dai hukumomin tsaro a jihar, sun dakatar da al'ummar musulmai zuwa wasu masallatan Idi a Jos, da kuma Barikin Ladi, don haka na tambayi kakakin gwamnatin jihar Filato Yiljab Abraham ko wasu matakai gwamnati ke dauka dangane da haka, sai ya ce:

"Gwamnatin Filato ta kafa kwamitin, da zarar ya gabatar da rahotonsa, majalisar tsaron jiha za ta duba wannan batu don a sami masalaha."

Ya zuwa yanzu dai jama'a na ci gaba da shirye-shiryen babbar Sallah inda ko-ina ka duba ba a birnin Jos da kewaye, babu abinda kake gani sai yadda jama'a ke hada-hada game da shirye-shiryen babbar Sallah. Da fatan za a yi sallar cikin lumana, da kwanciyar hankali.

Mawallafi: Abdullahi Maidawa Kurgwi
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin