Matakan tsaro a filin saukar jiragen sama na Dusseldorf
December 29, 2010Babban daraktan filin saukar jiragen sama na Dusseldorf da ke nan Jamus ya gabatar da wasu shawarwari da zumar ƙarfafa matakan tsaro a filayen saukar jiragen sama na Jamus.
Christoph Blume ya ce ta la´akari da yadda a ka kasa shawo kan matsalar tsaro , nan gaba kamata ta yi, a dinga ware fassenjoji rukuni -rukuni.
To saidai wannan shawara ta ci karo da mummunar adawa daga gwamnatin Jamus.
A yayin da ta ke hurucu akai, ministar suhurin kasar Jamus, Sabine Leutheusser-Schnarrenberger, ta ce wannan mataki ba zai aikatu ba, domin zai cusa wariya tsakanin fasenjoji, kuma ya sabawa ƙa´idodin Ƙungiyar Tarayya Turai da na Jamus game da batun nuna adalci tsakanin ko wane jinsi na bani adama, ba tare da la´akari da addininsa, ƙabilarsa ko kuma launin fatarsa ba.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu