1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Ruwanda ta karfafa wa mata gwiwa

Antonio Cascais, ZMA
March 8, 2019

Ruwanda ta kasance kasa daya tilo a nahiyar Afirka da ta kafa tarihi wajen karfafa mata, tare da ba su 'yancin taka rawa a gwamnati daidai da takwarorinsu maza.

https://p.dw.com/p/3EfWA
Ruanda Präsident Paul Kagame mit den neuen Parlamentsmitgliedern
Hoto: Getty Images/AFP/C. Ndegeya

Shekaru 25 bayan kisan kare dangi Ruwanda na a  matsayi na shida a duniya idan a kan batun daidaito tsakanin maza da mata, a yayin da tarayyar Jamus tana can baya a mukami na 14.Tun a shekara ta 2005 ne dai Ruwandan ta kaddamar da wani tsari na bai wa mata wani kaso mai tsoka a cikin kudin tsarin mulkin kasar, wanda zai ba su damar hawa wasu mukami na gwamnati. A karkashin tsarin mulkin kasar dai, an kebewa matan kashi 30 daga cikin 100 a kowane fanni. Kashi 60.1 na 'yan majalisar wakilai na kasar mata ne, wannan matsayi na matan ya kafa tarihi a duniya. A kasashen da suka ci gaba na duniya kamar Jamus, matan sune kashi 30.7 kacal. Sai dai duk da haka da sauran rina a kaba na cimma abin da aka sa a gaba a cewar 'yar kasuwa kuma mai shafin blog na Internet Natacha Umutoni.."Zan iya cewar muna kan hanyar isa wurin, ko shakka babu ba zan iya cewar komai namu na tafiya daidai ba, duk da cewar kashi 50 na majalisar ministocinmu mata ne. A nawa ganin, wannan misali ne mai kyau, amma har yanzu da sauran tafiya a wasu fannonin." Ita ma kakakin majalisar wakilan Ruwandan Donatille Mukabalisa na mai ra'ayin cewar duk da wannan matsayi da kasar tasu take, lamarin ba mai sauki ba ne da kasancewar da sauran rina a kaba.