Mata ministocin harkokin waje
Shugabar jam’iyyar The Greens Annalena Baerbock yanzu a hukumance ita ce farkon Bajamushiya ministar harkokin waje. Amma fa a wasu sassan duniya tuni mata ke rike da manyan mukaman diflomasiya.
Takardar nadi a fadar shugaban Jamus
Yanzu dai ta tabbata: Awace a karon farko ta tsaya takarar shugabancin gwamnatin Jamus Annalena Baerbock, shugaban kasa ya nada ta ministar harkokin waje. Jagorar jam’iyyar The Greens ce mace ta farko da ta rike mukamin, kuma mai shekaru 41 ita ce mafi karancin shekaru da ta rike mukamin. Ta ce tana son kyautata tsarin harkokin waje ga mata.
Sakatariyar waje daga Washington
Tun shekaru 20 da suka wuce Amirka ta fara nada mace ta farko a matsayin sakatariyar harkokin waje. Madeleine Albright, wace ta yi aiki da Bill Clinton, ita ce ginshikin sasanta rikicin Sabiya da Kosovo-Albaniya a 1999 a Paris. Takwaranta na Jamus a wancan lokacin dan jam’iyar The Greens ne Joschka Fischer.
Ayorkor Botchway: minista a Ghana
Tun shekaru baya kasashen Afirka suka fara nada mata ministocin harkokin waje. Yanzu haka a Ghana, Shirley Ayorkor Botchway ce babbar jami’ar diflomasiya. Ana iya ganinta a nan lokacin ziyara a Istanbul 2020. Tun a shekara ta 1979 aka nada mace ta farko ministar harkokin waje a yammacin Afirka.
Aiki tsakanin Gabas da Yamma
Netumbo Nandi-Ndaitwah ta kasance ministar harkokin wajen Namibiya kusan shekaru 10. Lokacin yakin wariyar jinsi ta yi aiki a Tarayyar Soviet da Birtaniya. Bayan samun yancin kan kasarta ta zama ‘yar majalisar dokoki. Sai kuma ta zama ministar harkokin waje tun a 2012. A nan, Nandi-Ndaitwah na karban bakunci ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a Windhoek.
al-Mangusch ta yi minista a Libiya
Batu mai ko yaushe shi ne abun tattaunawa idan Najla al-Mangusch ta karbi baki. Lauyar ‘yar shekaru 48 ita ce ministar harkokin wajen Libiya. Daya cikin mahimman kasashen duniya masu man fetur. Amma kuma arzikin man shi ne babban sanadin yakin basasan kasar. A nan, al-Mangush ta karbi bakunci ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu.
Tare da tattoo na gargajiya a ma’aiktar harkokin waje
Nanaia Mahuta ta kasance ministar harkokin wajen New Zealand tun Nowamba 2021, bayan ta rike mukamin ministar raya yankin Maori. Matan Maori zuriya da ke gauraye, a yanzu sun samu damar da ke kusa da su a cewar, Mahuta. Mukamin “babbar gata ce” ta ce. ‘Yar shekaru 50 da haifuwa ita ce mace ta farko a majalisar dokokin New Zealand da ke da tattoo a haba na gargajiya.
‘Yar Sweden mai rajin Turai
An dauke ta a matsayin mai neman mukamin shugabar gwamnati: mai kwarjini ministar harkokin wajen Sweden Anna Lindh. Amma a Satumban 2003, wani mai kisan gilla ya daba mata wuka a kantin sayar da kayayyaki a Stockholm, wanda ya kawo karshen rayuwarta ba zato ba tsammani. A yanzu, wata gidauniya mai sunan Anna Lindh na habaka tattaunawa tsakanin EU da sauran kasashen da ke kan iyaka da Bahar Rum.
"Zakanyar kasar Isra'ila"
Tun kafin kafuwar kasar Isra'ila, Golda Meir ta tattauna da sarkin Jordan don hana yakin Larabawa da Isra'ila - wanda bai yi nasara ba. A shekara ta 1956, ta zama ministar harkokin wajen sabuwar kasar, kuma a shekarar 1969 ta samu mukamin firaminista. Shin Annalena Baerbock, wacce kwanan nan ta nemi shugabancin Jamus, za ta sami irin wannan dama?