Mata 10 da suka yi fice a kwallon kafa
Mata 'yan kwallo a Jamus sun shirya bude kakar wasanni na 2019, da buga wasan sada zumunci da Faransa mai masaukin gasar kofin duniya. Ga fitattun 'yan wasa 10 da FIFA ta zaba a 2018 da lambar yabo ta Ballon d'Or.
Ada Hegerberg - 'Yar wasar da ta fi kowa iya taka leda
'Yar wasan gaba ta Norway ta shiga tarihi a 2018 bayan ta zama mace ta farko da ta samu lambar yabo ta Ballon d’Or. Mai shekaru 23 ta isar da sakon karfafa gwiwa ga yara mata matasa: "Don Allah ka yi imani kan abun da za ka iya." 'Yar wasan da ta fi kowa iya taka leda, Hegerberg ta zura sama da kwallo 250 a raga da yin nasara a gasar cin kofin Turai sau uku.
Pernille Harder - Shahararriyar mai jefa kwallo a raga
Wasan karshe na cin kofin Turai a 2017: 'Yar wasan gaba ta Denmak Pernille Harder ta sako kwallon a gaba, ta kauce wa mai tsaron gida tare da jefa kwallo a cikin raga wanda ya daidaita ci 2-2 a wasan da Denmak ta kusan yin asarar 4-2. Irin wannan kwarewa ce ta sa 'yar wasan gaba ta Wolfsburg zama wadda tafi kowa zura kwallo a raga a wasan Bundesliga na mata na 2017-18 kuma gwarzuwar UEFA.
Wendie Renard: Bajintar kare gida, laifi ne mai ma'ana'
Wendie Renard ita ce jarumar Olympique Lyon da tawagar mata 'yan kwallon Faransa. Da kwarewarta a wasan baya da jefa kwallo a raga da kai, ta samu lambar yabo a Faransa sau 12 da gasar kasashen Turai sau biyar. Ana yi wa Renard kallon 'yar wasan baya da ta fi kwarewa a duniya, da alkawarin zama jigo na Les Bleues domin samun nasarar lashe gasar cin kofin duniya ta mata a gida a 2019.
Lucy Bronze - 'Yar wasan baya mai karfin hali
Fitacciyar 'yar wasan baya ta Olympique Lyon Lucy Bronze ta kara da tsohon kulob dinta wato Manchester City, a gasar mata ta cin kofin Turai, a wasan kusa da na karshe Inda ta samu lambar yabo ta wadda ta fi jefa kwallo a raga ta kakar wasannin. Ana yi wa Bronze kallon daya daga cikin fitattun 'yan kwallo na duniya, da ake gani za ta taka leda wa Ingila a gasar cin kofin duniya ta 2019.
Marta Vieira da Silva: 'An haifeni don in yi amfani da wannan basirar'
"Yaki rashin goyon baya. Yaki da dukkansu — 'yan mazan, da kuma wadanda suka ce ba za ki iya ba," Wadannan su ne kalaman da Marta ta rubuta a kan labarin da aka rubuta kan karrama 'yan wasa. Da wannan manufa ta jefa kwallo a raga har sau 110 a wasanni 133 wa Brazil, ana yi wa Marta lakabi da zakarar mata a fagen wasanni mai abun koyi ga 'yan mata a kwallon kafa.
Dzsenifer Marozsan - Dawowa daga jinyar kumburin jijiyoyin zuciya
A watan Yulin da ya gabata ne dai tsohuwar kaftin din ta Jamus kuma tsohuwar 'yar wasan tsakiya ta Olympique Lyon ta gamu da larurar kumburin jijiyoyin zuciya. Amma a watan Oktoba ta koma kulub dinta, kafin ta sake hadewa a kungiyar kwallon kafa ta kasa. Marozsan ta yi fice wajen tsara kwallo ga 'yan wasan gaba. Tana daya daga cikin fitattun 'yan wasa uku na Jamus.
Amandine Henry - 'Yar wasan tsakiya mai wayo
Kusan kowane motsi aka yi za a yabeta 'yar wasan tsakiya ta Faransa Amandine Henry (sama ta hannun dama). Ta yi tasiri wajen sha wa Faransa kwallo a kulob dinta watau Lyon. Yadda take iya karanta tsarin wasan ya sa ake wa Henry kallon daya daga cikin fitattun mata 'yan kwallon kafa a duniya.
Samantha Kerr –Mai juyin biri
Samantha Kerr tana da tarihin jefa kwallo a raga sau 50 a wasannin lig-lig na cikin gida a kwallon kafar mata a Amirka. Kerr na 'yar shekaru 15 da ta fara kafa tarihi a babbar kungiyar kwallon kafa ta mata a Ostireliya tun daga lokacin ta jagoranci kungiyar zuwa mataki na shida a FIFA da share fagen shiga gasar cin kofin duniya na mata a 2019. Juyin biri shi ne alamar nasararta.
Megan Rapinoe - Fitacciya kuma mai fafutuka
Winger Megan Rapinoe ta taimaka wa Amirka nasarar cin kofin SheBelieves na 2018, da kofin duniya na 2015, kana da zinariya a wasannin Olympics na 2012. Kaftin ta Seattle Reign FC ta jefa kwallo 12 a raga a wasanni 18 a 2017. Mai shekaru 33 da haihuwa ta zama abun koyi ga yara mata, domin a yaki da nuna wariya, inda take ba da gudunmawar kashi daya na kudinta don wannan fafutuka.
Saki Kumagai - Tauraruwar Japan
Kaftin din ta Japan ta lashe wasanni biyar na Faransa da wasanin zakaru sau uku a jere da kungiyar Olympique Lyonnais. Basirar Kumagai a matsayin 'yar wasan baya ta taimaka wa Japan lashe kofin gasar yankin Asiya a 2018. Ta samu nasarar jefa kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan karshe da Amirka a gasar kofin duniya na 2011. A 2018 ta samu lambar yabo ta 'yar wasa da ta fi kwarewa.