1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga ta gawurta a Lebanon

October 18, 2019

An kwashe kwanaki biyu jere ana ci gaba da zanga-zangar neman gwamnatin Lebanon karkashin Firaminista Saad Hariri ta yi murabus.

https://p.dw.com/p/3RWYh
Libanon Proteste gegen Steuererhöhung und Korruption in Beirut
Hoto: DW/D. Hodali

Dubban masu zanga-zanga a birnin Beirut fadar gwamnatin kasar Lebanon da wasu sassan kasar sun kassara harkokin yau da kullum inda suke neman gwamnati ta yi murabus saboda matsalolin tattalin arziki da suka rincabe a kasar.

Wannan ke zama zanga-zanga mafi muni tun shekara ta 2015, kuma lamarin na kara tabarbara lamura a kasar da nuna alamar wargajewa. Firaminista Saad Hariri ya soke taron majalisar zartaswa da aka tsara a wannan Jumma'a domin duba yanayin da ake ciki. Kana a cikin kasafin kudin shekara ta 2020 mai zuwa gwamnatin ta Lebanon ta kirkiro da karin kudaden haraji kan taba sigari, da gas kafofin sada zumunta na zamani.

Ofishin jakadancin Kuwait da ke kasar ya gargadi 'yan kasar su yi a hankali sakamakon zanga-zanga da ke wakana. Kana ofishin jakadancin kasar Masar ya bukaci 'yan kasar kada su shiga wannan zanga-zanga.