Masu kishin addinin sun sare kan wani mutumin a Mali | Labarai | DW | 24.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu kishin addinin sun sare kan wani mutumin a Mali

Ƙungiyar Aqmi ta hile kan Wani buzu a arewacin Mali a birnin Timbuktu, tare da sako wasu mutanen guda huɗu da ta yi garkuwa da su.

Wani ɗan uwa ga mutumin da ya mutu ya ce an taras da gawarsa cikin daji an sare masa kai a arewacin birnin Timbuktu. Kuma ya ce bisa ga dukkan alamu Ƙungiyar Aqmi mai alaƙa da Ƙungiyar Al-Qaida ita ce ke da alhaki.

Aqmi dai na zargin mutumin da yi wa sojojin Faransa da na Majalisar Ɗinkin Duniya leƙen asiri. Ya zuwa yanzu hukumomin ƙasar ta Mali ba su mayar da martani ba dangane da wannan al'amari ba,haka ita ma rundunar sojojin Faransa.