Masu fyade za su bakunci lahira a Afghanistan | Labarai | DW | 07.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu fyade za su bakunci lahira a Afghanistan

Wadanda suka aikata wannan mugun aiki na fyade sun yi shi ne lokacin da matan suke dawowa da amare birnin Kabul bayan bikin daurin aure.

Calvin Gibbs

A gobe Laraba ne wasu mutane biyar 'yan asalin Afghanistan za su bakunci lahira ta hanyar rataya, bayan wani gangami da suka yi wajen aikata fyade ga wasu mata hudu, hukuncin da ke ci gaba da samun suka daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama a wannan kasa da ke fama da hare-haren na masu kunar bakin wake.

A makon da ya gabata ne dai kafin mika mulkin kasar, tsohon shugaban kasar ta Afghanistan Hamid Karzai ya rattaba hannu kan hukuncin kisa ga wadannan mutane da tun da fari ya bukaci a kashe su ta hanyar rataya kafin ma su je gaban kuliyar.

Guggun masu aikata fyaden sanye da kayan 'yan sanda sun tsaida motar amare lokacin da suke dawowa birnin Kabul bayan kammala wani bikin daurin aure.

Har ila yau maharan bayan da suka daure maza daga cikin tawagar, sun aikata fyade da akalla mata hudu cikin tawagar, tare da sace musu wasu kayayyakin su masu muhimmanci. Dukkanin masu fyaden biyar an same su da aikata wannan laifi a wata shari'a da aka yi musu da ta dauki tsawon sa'oi biyu da aka yada ta kai tsaye ta kafar talabijin a kasar, hukuncin da kotun daukaka kara da kotun koli suka amince da shi ba tare da bata lokaci ba.