1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona na tu'annati a Afirka

January 10, 2021

Yawan mutanen da cutar Corona ta hallaka a nahiyar Afirka ya kai dubu 72.

https://p.dw.com/p/3nlHB
Coronavirus Südafrika | Klinik mit Covid-19 Station
Hoto: RODGER BOSCH/AFP

Cibiyar kula da cututtuka masu saurin yaduwa ta Afirka ta ruwaito a ranar Lahadin nan cewa, nahiyar ta kai matakin samun mutane sama da miliyan uku da suka kamu da cutar Corona, yayin da wasu sama da dubu saba'in da biyu suka mutu.

Kasar Afirka ta kudu na kan gaba da kaso 30 cikin 100 na masu dauke da cutar a nahiyar, wanda ake ganin haka na faruwa ne sakamakon gwajin cutar da kasar ke yi akai-akai.

Shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya shirya wani zama na musamman da manyan jami'an gwamnatinsa, domin duba yiwuwar tsaurara matakan rage yaduwar annobar.

Gaba kadan a cikin wannan watan da muke ciki ne ake sa ran kasar za ta fara bayar da rigakafin cutar, wadda kamfanin harhada magunguna na AstraZeneca zai samar.