1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu ayyukan ceto a Indonesiya na fuskantar kalubale

Salissou BoukariAugust 17, 2015

Rishin kyawon yanayi na haifar da cikas a kokarin da masu ayyukan ceto ke yi na isa wani yankin mai tsaunuka inda aka gano baraguzan jirgin da ya fadi a Indonesiya.

https://p.dw.com/p/1GGgt
Inda aka gano baraguzan jirgin
Inda aka gano baraguzan jirginHoto: Reuters/ Indonesia's National Search and Rescue Agency

Jirgin dai na kamfanin Trigana na kasar ta Indonesiya ya bace ne a ranar Lahadi tsakanin wasu birane biyu na kasar da ke cikin jihar Papouasie a Arewacin kasar dauke da mutane akalla 54. Wannan dai shi ne karo na uku da ake samun hadarin jirgin sama a wannan kasa ta Kudancin Asiya a kasa da shekara guda wanda hakan ke sanya kara aza ayar tambaya kan batun lafiyar jiragen kasar. Akalla dai jami'an tsaro 250 ne tare da sauran masu ayyukan ceto ke kokarin samar da wata hanya cikin wani kungurumin daji domin su samu isa inda hadarin ya aufku. Sai dai kuma kawo yanzu ana da babban shakku na samun wani mai rai a wannan hadari.