Masaƙu a ƙasar Bangladesh na shirin bada kai
November 14, 2013Talla
An sake buɗe masaƙu a ƙasar Bangaladesh bayan zanga-zangar da ma'aikata suka yi bisa neman ƙarin albashi. Dama dai sama da masuƙu 200 ne suka rufe aikinsu, kafin Firaministar ƙasar Sheikh Hasina ta shiga tsakani. Wasu kamfanonin da suka gana da Firaministar, sun amince su yi wa ma'aikatan ƙarin albashi na kashi 77 cikin ɗari, inda yanzu albashin lebura ya kai dalar Amirka 66 a wata, wato kwatankwacin Naira dubu goma kacal. Gwamnatin ƙasar dai ta kafa kwamitin da ya amince da wannan ƙaramin albashin, amma shi ma wasu kamfanonin sun ƙi biya, Duk da cewa ƙasar ita ce mafi ƙanƙantan albashi a duniya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Saleh Umar Saleh