Marubutan shirin “Masu Yaƙi da Muggan Laifuka“ | Masu Yaki da Muggan Laifuka | DW | 24.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Yaki da Muggan Laifuka

Marubutan shirin “Masu Yaƙi da Muggan Laifuka“

Mutane da yawa sun yi aikin hadin gwiwa wajen tabbatar da nasarar wannan wasan kwaikwayo na "Masu Yaƙi da Muggan Laifuka".

Pinado Abdu Waba ta fara aikin jarida ne bayan kammala karantunta a wannan fanni a garin Zaria da ke arewacin Najeriya. Daga nan ne ta ci gaba da aiki a matsayin mai dauko rahotanni ga gidan talabijin, inda daga bisani ta sauya sheka zuwa wata jarida mai fitowa a ko wace rana a Najeriya. Ta kasance mai sha'awar fasahar rubuce-rubuce. Sai dai bata cimma wannan buri ba har sai da ta fara aiki a gidauniyar horas da ma'aikatan jarida na BBC Media Action, inda takan rubuta wasannin kwaikwayo cikin Hausa da Turanci. Wadannan wasannin kwaikwayo sukan tabo muhimman batutuwan rayuwa kamar shugabanci na-gari, kiwon lafiya da dai makamantansu. Pinado ta fara aiki da sashen Hausa na DW a shekara ta 2010 a matsayin Edita. "Yan ra'ayin rikau" shi ne gudummawarta ta farko a jerin shirye-shiryen "Masu Yaki da Muggan Laifuka".

James Muhando shahararren mai nishadantarwa ne a kasar Kenya, wanda yake aikin rubuce-rubuce tun daga shekara ta 1999. Ya fara aikin nasa ne a matsayin mai bayyana a dandali, kafin daga bisani ya hade da kafar yada labaru na kasar Kenya a matsayin marubuci da kuma mai wasan kwaikwayo a talabijin da rediyo. Shahararren mai gabatar da shirye-shirye na gidan talabijin da rediyon na Kenya, ya shiga ayarin 'yan wasan kwaikwayo na shirin "Ji Ka Karu" na DW ne a shekara ta 2008, a matsayin dan wasa. Shi ne ya rubuta wasan kwaikwayon "Yan farauta-dadi" a bangaren shirin "Masu Yaki da Muggan Laifuka". Kazalika James ne ya rubuta wasan kwaikwayon nan na "Hadarin karbar bashi" da kuma "Tsaka mai wuya" zubi na daya da na biyu da kuma na uku. Bugu da kari ya taimaka wajen shirya wasan "Yaki da Muggan Laifuka" a birnin Nairobi.

Chrispin Mwakideu dan asalin kasar Kenya ne, wanda ke da basirar yin zane-zanen hotuna da kuma amfani da 'yartsana wajen fadakarwa da illimantarwa, kana ya yi fice a yin wasa da rubuta wasannin kwaikwayo. Ya dauki tsawon lokaci yana amfani da irin wadannan zane-zane da hotunan 'yartsana wajen shawo kan matsalolin rayuwa da siyasa da tattali. A gareshi dai rubuta wasannin kwaikwayo na rediyo, tamkar tafiya ce mai nishadi. Ya ce baya ga jin dadin abunda yake rubutawa, yakan koyi darussa masu yawa. Chrispin shi ne ya rubuta "A garin Danya" wanda daya ne daga wasannin kwaikwayon "Masu Yaki da Muggan Laifuka". Shi ne ya rubuta zangon farko na "Tsaka mai wuya". Kazalika ya rubuta shirye-shiryen "Ji ka Karu" da suka hadar da "Shiga harkokin siyasa" da "Yaki da cutar Malaria" da kuma wasan kwallon kafa a Afirka.

An haifi Mukoma wa Ngugi a Evanston, Illinois a can kasar Amirka, kuma ya girma ne a Kenya kafin daga bisani ya koma Amirka da zama. Fitaccen marubucin Afirkan nan Ngugi wa Thiong ne mahaifinsa kuma malamin koyar da Turanci ne a jami'ar Cornell. Ya rubuta litattafai masu yawa. Mukoma ne ya rubuta wasan "Ga Maganin Waraka ga na Kisa". Daya daga cikin wasannin kwaikwayon "Masu Yaki da Muggan Laifuka". Ko shakka babu wannan marubuci ya yi suna a rubutun wasannin rediyo.

Fitattun marubutan adabi a fannin muggan laifuka Helon Habila (Najeriya) da Andrew Brown (Afirka ta Kudu) suka tallafa wa shirin a matsayin masu bayar da shawarwari.