1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Peru ya yi murabus

Suleiman Babayo
March 23, 2018

Majalisar dokokin Peru ta amince da murabus na Shugaba Pedro Pablo Kuczynski inda mataimakinsa tsohon gwamna wani lardi Martin Vizcarra ya dauki madafun iko.

https://p.dw.com/p/2ustY
Peru Martín Vizcarra
Hoto: Reuters/G. Pardo

Majalisar dokokin kasar Peru ta amince da murabus da Shugaban kasar Pedro Pablo Kuczynski ya yi, abin da zai share hanya ga mataimakinsa tsohon gwamna wani lardi Martin Vizcarra ya dauki madafun iko a wannan kasa da ke yankin Latin Amirka.

Kuczynski ya zama shugaban kasa na farko da ruwan rikicin zargin cin hanci da wani kamfanin Brazil ya yi awun gaba da shi. Sai dai sabon Shugaba Martin Vizcarra na kasar ta Peru yana da gagarumin kalubale a gaba kan yaki da cin hanci da daidaita tattalin arzikin kasar.