Martanin ′yan Najeriya bisa soke wasu hukumomi | Siyasa | DW | 03.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin 'yan Najeriya bisa soke wasu hukumomi

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta soke hukumomin jarrabawa kamar su NECO da IJMB da sauransu

HANDOUT - Mädchen in Niger, die sich freuen, eine Schule besuchen zu dürfen, halten kleine Tafeln, auf denen «11. Oktober» geschrieben steht, in ihrem Klassenzimmer hoch (undatiertes Foto). Die internationale Hilfsorganisation «Plan» hat die Vereinten Nationen davon überzeugt, dass die Welt auch einen Weltmädchentag braucht. Denn Mädchen werden in vielen Ländern benachteiligt und haben nicht die gleichen Chancen wie Jungen. Der Tag ist für alle Mädchen weltweit, also auch für die Mädchen in Deutschland. Foto: Plan International - ACHTUNG: Nur zur redaktionellen Verwendung und nur mit Nennung der Quelle: «Plan International» +++(c) dpa - Bildfunk+++

Wasu dalibai cikin aji

A kokarin da gwamnatin shugaba Goodluck tace tana yi na tsimin kudi ta amince da rufe wasu hukumomin gwamnati irinsu NECO mai shirya jarabawan gama sakandare da kuma hukumar kawar da talauci ta kasa NAPEP. Sai dai yan Najeriya sunce akwai lauje cikin dadi game da matkin na gwamnati. kamar yadda wannan ɗalibin ke cewa.

“A gaskiya wannan labari da muka ji bai mana dadi ba, domin yawancin dalibai na samun madogara, idan basu ci WAEC ba, za su ci NECO, kuma idan aka ce an soke NECO, akwai matsalar samun shiga jami'a”

A baya bayan nan ne dai gwamnatin ta Najeriya ta kafa wani kwamiti a karkashin tsohon shugaban ma'aikatan kasar Steven Orasanya na rage wasu ma'aikatu da kuma hade wasun su, domin tsimin kudi da kuma aiki tukuru. To ko yaya iyayen yara suka ji game da wannan mataki da gwamnatin ta dauka? gadai Alhaji Usman Musa Kasuwan Garba.

Nigeria's President, Goodluck Jonathan and Dame Patience Jonathan, his wife, wait for him to collect a certificate of return as the next President , in Abuja, Nigeria, Tuesday, April 19, 2011. The mobs poured into the streets by the thousands in this dusty city separating Nigeria's Muslim north and Christian south, armed with machetes and poison-tipped arrows to unleash their rage after the oil-rich nation's presidential election. (AP Photo/Felix Onigbinde)

Shugaba Goodluck Jonathan da uwar gidansa Dame Patience

"A gaskiya matakin da gwamnati ta ce ta dauka bai dace ba, na farko akwai ma'aikata dake aiki a wadanan hukumomi, kuma jarrabawan NECO ya taimaka wa dalibai samun shiga jami'a. A maimakon dogaro da WAEC, kaga idan gwamnati ta soke NECO an maida hannun agogo baya kenan"

A rahoton da kwamitin ta Orasanya ta bayar dai, ta bada shawarar soke hukumar shirya jarrabawan kammala sakandare ta NECO, ko kuma a hade ta da hukumar WAEC, wanda tun farko ita aka sani wajen shirya jarrabawan kammala sakandare da kuma hade hukumar shigar da koke koken jama'a da hukumar kare hakkin bil'adama ta kasa, sai kuma hukumar kawar da talauci ta kasa wato NAPEP da kuma hukumar shirya jarrabawar shiga jami'a ta IJMB da hukumar JAMB ke gudanarwa.

Koda yake kokarin da na yi don jin ta bakin shugaban hukumar ta NECO a ofishinsa dake birnin Minna ya citura, inda wata majiya ta shaida mani cewar baya ofis. Sai dai malam Yahaya Sule wani dalibine da ya kammala sakandarensa kuma na yi kicibis da shi a bakin kofar shiga hukumar ta NECO, Inda ya shaida mani bacin ransa da yadda suka ji game da wannan labari.

Schülerinnen in einer Grundschule in Bauchi / Nordnigeria. Copyright: Thomas Mösch

Wasu daliban a Bauchi

Duka duka dai hukumomi 38 ne za'a rufe, kana a hade 52 tare da wasu, kana kuma a maida 14 zuwa ma'aikatun da suka fito tun farko.

A cewar gwamnati dai wannan mataki da ta dauka zai taimaka mata wajen tsimin kudi har Naira biliyan 862 a cikin shekaru 3 masu zuwa, abinda kuma iyayen yara irinsu Alhaji Usman Kasuwan Garba ke ganin ba'a yi wa talakawa adalci ba, kuma an bar Jaki ne kawai ana dukan tanki.

Bayan Hukumar shirya jarrabawan NECO da gwamnati za ta dakatar akwai hukumar kawar da talauci ta kasa wato NAPEP wanda ke samar da jari da kuma baburan hawa da aka fi sani da keke NAPEP domin kawar da talauci. Dukkannin hukumomin na NECO da NAPEP dai an kafasune a zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, abinda ya sa wasu ke ganin akwai lauje cikin nadi game da matakin na gwamnati.

Tuni dai kungiyar kwadago ta kasar ta tsare tare da gargadin gwamnati da ka da ta kuskura ta sallami ma'aikatan wadanan hukumomi data soke, a abinda kungiyar ta kira lamarin da basuji, ba su gani ba.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin