Martanin shugabanni kan harin ta′ddanci a London | Duka rahotanni | DW | 04.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

Martanin shugabanni kan harin ta'ddanci a London

Akalla mutane bakwai suka mutu bayan wani harin ta'addanci da aka kai da mota a gadar birnin London, kasa da makonni biyu da harin kunar bakin wake a Manchester da ya hallaka mutane 22.

Shugaba Trump na Amirka ya kasance a sahun gaba a jerin shugabannin duniya da su ka yi tir da Allah wadai da wanann hari na birnin London inda da farko a shafinsa na Twitter ya wallafa cewa duk abin da ya dace Amirka ta yi domin kawo goyon bayanta da gudunmawarta ga Birtaniya a shirye take ta yi shi, kafin daga bisani ya kira Firaministar kasar Theresa May ta wayar tarho ya jaddada mata goyon bayansa dari bisa dari, kana daga karshe fadar White House ta fitar da sanarwa inda ta yi tofin Allah tsine kan harin da ta ce an  kai kan fararan hula da ba su ji ba basu gani ba, wanda ta bayyana da cewa abin kunya ne.

Ita ma dai Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a cikin wata sanarwa da ta fitar, bayan gabatar da ta'aziyyarta ga al'ummar Birtaniyar, ta kuma bayyana takaicinta da afkuwar harin wanda ta ce ba zai sa su yi kasa a gwiwa ba wajen yakar duk wani nau'i na ta'addanci ko daga ina ya fito. A nasa bangare Shugaba Emmanuel Macron na Faransa wanda ya tabbatar da jimuwar Faransawa hudu a cikin harin na birnin London ya ce Faransa za ta kasance a ko da yaushe a tare da Birtaniya a cikin yaki da ta'addanci.

Theresa May Ansprache London (picture alliance/dpa/A.Matthews)

Firaministar Birtaniya Theresa May

Ita ma dai kasar Rasha ta bakin ministan tsaronta Alexander Fomin da ke halartar wani taron harakokin tsaro da ke gudana a yanzu haka a Singapour ta soki lamarin harin na birnin London.

"Ya ce ina mika babbar ta'aziyyata ga mutanen da suka mutu a wannan hari da ma wanda aka kai a birnin Manchester, da a kasar Phillipine da Indunusiya da a sauran kasashe, domin duk wadannan bala'o'i da ke afkuwa abin daukar darasi ne"

Shi ma dai Ministan tsaro kasar New Zealand Mark Mitchell da ke halartar taron tsaron na Singapour cewa ya yi ba za su yi kasa a gwiwa  ba wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda.

"Ya ce mun san kungiyoyin 'yan ta'adda na ci gaba da neman goyon baya ta hanyar yin amfani da raunin tsaron da ke kan iyakokin kasashenmu, da kafofin sada zumunta na zamani. kuma wannan babbar barazanar tsaro ce da ke nuna mana cewa mu dukkanmu muna cikin hadari, domin wannan hari na birnin London wani babban tuni ne kan irin kalubalen da ke a gabanmu"

Wannan hari na birnin london na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan al'ummar kasar Birtaniyar su gudanar da zaben majalisar dokoki kuma magajin garin birnin na London Sadiq Khan ya bayyana harin da cewa wani yunkuri ne na neman hana gudanar da zaben.

London Bürgermeister Sadiq Khan (picture-alliance/AP Photo/K. Wigglesworth)

Magajin garin London Sadiq Khan

"Ya ce 'yan ta'adda na da burin hana mana gudanar da zaben ne da nufin yin illa ga demokradiyyarmu, mu kuma ba za mu taba basu wannan dama ba, kuma ba za mu ba su damar samun nasara kanmu ba"

Da misalin karfe tara da minti takwas na daran Asabar ce wasu mutane uku suka kai hari da babbar mota inda suka kutsa a guje cikin taron jama'a a kan gadar ta birnin London kafin daga bisani su shiga cikin gari suna daba wa jama'a wuka, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida a yayin da wasu kimanin 50 suka ji rauni. Wannan dai shi ne karo na uku a cikin wata uku da birnin na London ke fuskantar harin ta'addanci.