Martanin Isra´ila ga harbe-harben rokoki daga Labanon | Labarai | DW | 28.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin Isra´ila ga harbe-harben rokoki daga Labanon

Kasar Isra´ila ta maida martani, ga harbe harben rokokin da wasu mutane daga kasar Labanon su ka yi ga wannan sansanin sojan ta asahiyar yau lahadi.

Hukumomin Isra´ila sun bayyana sanarwar ɗora alhakin harin, ga gwamnatin Labanon.

Kazalika sun ce, za su shigar da kara gaban komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia.

Wani kakakin jami´an tsaron kasar Labanon, ya sanar cewa harin na Isra´ila, ya yi setinwasu rundunoni, mallakar yan tsatsauran ra´ayin Palestinu, da ke jibge a kasar. Sojoji 6, su ka ji mumunan raunuka, a sakamakon wannan hari.