1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan kasafin 2014 a Najeriya

April 10, 2014

Masana tattalin arziki na ci gaba da tsokaci kan kasafin kudi na Naira Triliyan 4.6 da majalisar datawan kasar ta amince, musamman kaso kan muhimman ayyuka.

https://p.dw.com/p/1Bfte
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Amincewa da kasafin kudin da majalisar datawan Najeriyar ta yi da ya nuna cewar majalisar ta yi karin Naira bilyan 53 a kan abin da shugaban Najeriyar ya gabatar mata watani hudu da suka gabata, inda a yanzu ‘yan majalisar suka sanya kasafin a kan adadin Naira triliyan 4.6 a wannan shekarar.

Ko da yake ana farin cikin matakin ya kawo karshen jan kafa da ma jinkirin da aka fuskanta a tsarawa da ma amincewa da kasafin kudin na bana, wanda a bana sashin ilimi ya samu kari a kaso na daya kai Naira bilyan 373.5 a kasafin da aka tsara shi a kan dala 77.50 na kowace gangar man fetir milyan 2.388 da kasar ke hakowa, amma ga Malam Abubakar Ali masani a fanin harkokin tattalin arzikin Najeriya na mai cewa har yanzu fa bata canza zani ba a game da batun kasafin kudin Najeriyar.

"Idan ka duba kasafin kudin kamar shekarun baya kason da aka dauka aka baiwa muhimman ayyuka bai fi kashi 27.30 ba kusan kashi 70 za'a kashe ne a kan harkokin yau da kullum. A maimakon halin da muke ciki na rashin muhimman abubuwa na hanyoyin motoci ne, na wutan lantarki ne da makarantu maimakon a duba irin wadannan ba haka aka yi ba. Saboda haka babbar matsala ce, to amma a ma aiwatar da shi wannan din da aka yi shi ne wahala, in an aiwatar da shi to, za mu yi masu kyakyawan zato".

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria ARCHIV 2013
Shugaba Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/AP Photo

Daukacin 'yan majalisar ne dai suka amince da wannan kasafin kudi to sai dai sanatocin da ke sashin arewa maso gabashin Najeriya sun yi korafin a kan rashin kari a kan Naira bilyan biyu da aka kebewa yankin nasu a matsayin kudin kai dauki saboda matsalolin rashin tsaro. Sanata Ahmed Lawan ya bayyana man abin da ya daga masu hankali.

"A kara zuwa wani abu wanda ya yi kama da adalci ya yi kama da gaskiya saboda a nemawa matasanmu ayyukan yi a cikin wannan kasafin kudi a wannan shekara badi ma in Allah ya kai mu sai a sake kwatawa, saboda muna da matasa da dama da basu da ayyukan yi, kuma a cikinsu ne ake samun wadanda ke shiga rudani, domin hannu da bashi da abin yi ba shakka duk abin da aka kawo mishi karba zai yi".

Zargin rashin aiwatar da kasafin kudi dai na zama daya daga cikin babbar matsalar da ake fuskanta a Najeriya, domin ko a bara an ta kai ruwa rana a tsakanin yan majalisar da bangaren zartaswa. Amma ga Malam Dantani Dio Zuru na kungiyar nuna goyon baya ga shugaba Jonathan ya ce ya kamata fa a yaba yadda lamuran suke.

National Assembly in Abuja, Nigeria
Hoto: DW

"Kusan komai ya yi dai dai game da batun kasafin kudin domin babu ma wanda ya sa ran za'a amince da kasafin kudin nan a yanzu saboda 'yan mahawarori da suka taso a majalisar. Kuma duk dan Najeriya ya san cewa komai aka bi shi a hankali za'a cimma iyakarsa don waannan kasafin kudin ya yi dai dai bisa ga tsari".

Abin jira a gani shi ne ko gwamnatin zata canza salonta wajen aiwatar da kasafin kudin sau da kafa kamar yadda shugaban majalisar datawan David Mark ya yi gargadi, musamman nuna tsoron da ake yi kan cewa shekarar zabe ce a gaban Najeriyar wacce bisa al'ada akan fukanci kashe kudadde bisa yanayi na kura ta tsere da na bakinta saboda cikar wa'adin mulki ga mafi yawan zababbun wakilai.

Mawallafi : Uwaisu Abubakar Idris
Edita : Zainab Mohammed Abubakar