Martani dangane da hukuncin kisa akan Sadam | Labarai | DW | 06.11.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martani dangane da hukuncin kisa akan Sadam

Ayayinda shugabannin gwamnatocin kasashen duniya ke cigaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yankewa tshon shugaban Iraki Sadam Hussein a jiya lahadi,an samu rarrabuwar kawuwa tsakanin kafofin yada labaru,akan wannan hukunci.Ayayinda wasu kafofin yada labarun kassashe ke maraba da wannan hukunci,wasu kuwa gargadi sukayi dacewa,aiwatar da wannan hukunci akan Sadam bazai haifar da komai ba,face dada jefa kasar Iraki cikin halin haulai.

Yini guda bayan zartar da wannan hukuncin kisa dai,masu nazarin lamuran dakan je suzo,sun fara bayyana shakku adangane da tasirinsa wa shugaba George W Bush,mutuminda ya jagoranci yakin da aka kadaamar akan Irakin a 2003,wanda kuma ke fuskantar bazaranar zaben yan majalisa a tsakiyar mulkinsa,a gobe talata a Amurka.Jaridar New York times alal misali,ta bayyana bukatar sake nazarin wasnnan hukuncin kisa da aka yankewa Sadam.Wasu jaridun kasashen yankin gabas ta tsakiya dai sai bayyana murna sukeyi,ayayinda alumman palasdinawa ke juyayin wannan hukunci,wa mutumin daya taimaka musu.

 • Kwanan wata 06.11.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu4w
 • Kwanan wata 06.11.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu4w