Sabon shugaban gwamnati a Maroko
September 11, 2021Talla
Sarkin dai ya karbi bakuncin Aziz Akhannouch tare da bukatarsa da ya kafa sabuwar gwamnati kamar yadda fadar ta umarta. Jam'iyyar Akhannouch ta Independent National Assembly da ke da sassaucin ra'ayi, ta lashe kujeru 102 cikin 395 na majalisar dokoki a yayin zaben 'yan majalisun dokokin da aka gudanar a Maroko a ranar Larabar da ta gabata. A cewar ma'aikatar harkokin cikin gida ta Marokon jam'iyyar PJD da ke kan karagar mulki tun daga shekara ta 2011 ta sha gagarumin kaye, inda ta samu mambobi 13 kacal a majalisar dokokin a wannan karon.