Maroko: Malamai sun yi zanga-zanga | Labarai | DW | 24.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Maroko: Malamai sun yi zanga-zanga

Malaman makaranta a kasar Maroko sun gudanar da wata sabuwar zanga-zanga a yau din nan don nuna rashin amincewarsu da yanayin da aiki na koyar yake a kasar.

Masu aiko da rahotanni suka ce kimanin malamai dubu goma ne suka hadu a Rabat babban birnin kasar, sa'o'i kalilan bayan da 'yan sanda suka tarwatsa gangamin da wasu takwarorinsu su ka yi. Yayin zanga-zangar dai, malaman makarantar sun yi tattaki daga ma'aikatar ilimin kasar zuwa wani babban dandali da ke tsakiya birnin na Rabat, inda su ka yi ta rera kalamai na nuna rashin amincewa da halin da sha'anin koyo da koyarwa ke ciki a kasar.