Maris 2016 ya zamo wata mafi zafi a shekaru 137 | Labarai | DW | 19.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Maris 2016 ya zamo wata mafi zafi a shekaru 137

Zafin da aka yi a saman doran kasa a watan Maris da ya gabata ya zarce duk wani zafin da aka taba fuskanta a cikin karni na 20 da digiri 1,22 a ma'aunin zafi na Celsius

Wani rahoto da wata hukumar kula da yanayi ta kasar Amirka ta wallafa a wannan Talata kan batun yanayin zafi a duniya ya nunar da cewa watan Maris da ya gabata shi ne ya kasance watan Maris mafi tsananin zafi a cikin shekaru 137 da suka gabata.

A takaice yanayin zafi da aka yi a duniya a cikin watan Maris na wannan shekara ta 2016 ya zamo zafi mafi tsanani da aka taba fuskanta a cikin watan Maris a tarihin bincike da hukumar take gudanarwa tun daga shekara ta 1880.

A jumulce a watan na Maris da ya gabata zafin da aka yi a saman doran kasa ya zarce duk wani zafin da aka taba fuskanta a cikin karni na 20 da digiri 1,22 a ma'aunin zafi na Celsius. Rahoton ya bayyana cewa wannan karuwar zafi da aka fuskanta na nuni da irin karuwar dumamar yanayi da duniya take fuskanta.

A watan Disamba da ya gabata ne dai kasashen duniya suka cimma wata yarjejeniyar takaice karuwar dumamar yanayi da digiri biyu a taron yanayi na duniya da ya gudana a birnin Paris.