Marafa Hamidou Yaya dan siyasa ne a Kamaru wanda ya taba rike mukamin ministan cikin gida da babban sakatare janar na fadar shugaban kasa.
Shi dan gidan sarauta ne na Garoua da ke arewain kasar, wanda a shekarun baya ya samu kusanci da shugaban kasar Kamaru Paul Biya. Sai dai sabani tsakaninsu da zargin cin hanci da karbar rashawa ya sa an yanke masa hukuncin dauri a gidan yari.