Manufofin yakin neman zabe a Jamus | Siyasa | DW | 02.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufofin yakin neman zabe a Jamus

A cikin shirye-shiryen zaben Jamus shugabar gwamnati Merkel ta fuskanci babban abokin hamayyarta Steinbrück, a wata muhawara ta telibijin.

A lokacin muhawarar da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da babban abokin hamayyarta a neman kujerar shugabancin gwamnati Peer Steinbrück suka gudanar, sun sami daidaiton ra'ayi dangane da rikicin Siriya, inda 'yan takarar biyu, suka ce Jamus ba za ta shiga a dama da ita ba, a duk lokacin da Amirka ta nemi jagorantar kaddamar da harin soji a kan Siriya. Merkel, ta ce in ma za ta yi hakan, to kuwa da sharadi:

Ta ce "Sam sam Jamus ba za ta shiga cikin duk wani matakin soji a kan Siriya ba. In ma za ta yi hakan, sai dai da kudirin Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar kawancen tsaron NATO da kuma na Kungiyar Tarayyar Turai. Sannan suna iya kokari, tunda har yanzu shirin yana gaban Majalisar Dinkin Duniya.

The top candidate of the Social Democratic Party (SPD) in the upcoming German general elections, Peer Steinbrueck, speaks during a news conference in Berlin, August 29, 2013. German voters will take to the polls in a general election on September 22. REUTERS/Thomas Peter (GERMANY - Tags: POLITICS ELECTIONS)

Dan takarar SPD, Peer Steinbrück

Rikicin kudi a Turai

Kazalika dangane da batun Girka ma , 'yan takarar biyu, wato Merkel ta Steinbrück, sun daidaita a kan yiwuwa baiwa kasar ta Girka rancen kudi a karo na uku domin ceto tattalin arzikinta. Sai dai babu ko daya daga cikinsu da ya bayyana kiyasin yawan kudin da kasar ta Girka ke bukata. Steinbrück dai ya zargi gwamnatin Merkel, da gazawa a kokarin warware matsalar koma bayan tattalin arzikin da wasu kasashen gamayyar Turai da ke yin amfani da takardar kudin Euro ke fama dasu. Dan takarar jam'iyyar ta SPD dai, ya kara da cewar, mahukunta a birnin Berlin, fadar gwamnatin Jamus sun bayar da fifiko a kan matakan tsuke bakin aljihu, inda kuma suka gaza mayar da hankali sosai a kan matakan farfado da tattalin arziki:

"Kamata yayi mu tuna cewar, wadannan kasashen na garzaya wa zuwa wajenmu domin tabbatar da hadin kan Turai, kuma tunda sun nuna farin cikinsu dangane da sake hadewar gabashi da yammacin Jamus, to, kuwa alhaki ne da ya rataya a wuyanmu mu taimaka musu, ba wai kawai ta hanyar matakan tsuke bakin aljihun gwamnatoci ba, dake sanya kasashen Turai da ke fama da rikicin kudi ke ci gaba da zama cikin matsala ba."

A nata bangaren, Merkel, ta kafa hujjar cewar, Jamus ta dauki matsayi ne na kasancewarta ginshikin bunkasar tattalin arziki a nahiyar Turai a zamanin mulkinta.

Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) winkt am 27.08.2013 während einer Wahlkampfveranstaltung in Rendsburg (Schleswig-Holstein). Foto: Carsten Rehder/dpa

'Yar takarar CDU, Angela Merkel

Badakalar leken asirin Amirka ga Jamus

Sai dai a lokacin da 'yan takarar biyu suka tabo batun leken asirin da Amirka ke yi wa Jamusawa a kasarsu ta haihuwa kuwa, Merkel ta yi watsi da zargin inda da ce:

"A wannan badakalar dai, anan ofis din, muna kare martabar Jamus. Mun yi ma Amirka da hukumar leken asirrinta tambayoyi, kuma sun bamu bayanan da suka samu daga mutanen da ke aiki a fadar shugaban Amirka ta White House. Saboda haka dole ne Jamus ta amince dasu, domin ba ta da wani dalilin karyatasu. Idan kuwa muka sami wata hujjar da ta taso daga baya, to a lokacinne za mu dauki mataki."

Sai dai kuma dan takarar jam'iyyar SPD, Steinbrück, ya zargi shugabar gwamnatin Jamus da sabawa rantsuwar kama aikin da ta yi na kare cutar da Jamus, bisa kyale hukumar leken asirin Amirka na sanya ido a kan sakonnin Jamusawa ta yanar gizo zuwa ketare.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin