Manufofin Jamus game da Afirka ta Yamma | Siyasa | DW | 02.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufofin Jamus game da Afirka ta Yamma

A kwanan nan tarayyar Jamus ta yi ta tura wasu ministocinta rangadi ƙasashen yammacin Afirka, ko hakan na nufin ƙasar na shirin samar da ƙwaƙkwarar manufa ga wannan yanki ke nan?

Idan aka dubi tafiye tafiyen da ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle da ministan raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel suka yi kwanakin nan a ƙasashen yammacin Afirka, za a ga cewa wannan yanki na ƙara samun muhimmanci a manufofin gwamnatin tarayyar Jamus.

Kawo yanzu babu wata manufar gwamnatin Jamus game da yankin yammacin Afirka. In ban da ɗaiɗaikun ma'aikatun gwamnati ko ƙungiyoyin agaji na Jamus dake aiki a ƙasashen yankin ba, inji Farfesa Ulf Engel masanin harkokin nahiyar Afirka a jami'ar birnin Leipzig.

"Ya zuwa wannan lokaci ba a da wata tsayayyar manufa game da wata ƙasa a yankin. Saboda haka a gani na duk wata manufar Jamus a kan yammacin Afirka ba za ta wuce irin manufar gwamnatin tarayyar Jamus game da gabacin Afirka."

Manufar rangadin yammacin Afirka

A farkon wannan mako ministan raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel ya fara ziyarar aikin mako guda a Kamaru inda a wannan ziyara ya tattauna da shugaban ƙasa Paul Biya. Sannan shi kuma ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya fara rangadin ƙasashen Mali, Senegal da tarayyar Najeriya. Bayan tattaunawa da shugabannin Najeriya an shirya kai ziyara a shelkwatar gamaiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yammam wato ECOWAS ko CEDEAO a birnin Abuja, inda wakilan ƙungiyar su 15 ke shawarwari game da ɗaukar matakan soji kan ƙasar Mali.

Westerwelle Mali Ankunft Reise Flugzeug Tiéman Hubert Coulibaly

Westerwelle lokacin da ya sauka a Mali

Halin da ake ciki a ƙasar ta Mali musamman arewacin ƙasar dake ƙarƙashin ikon ƙungiyoyi masu kaifin kishin addinin Islama, ka iya zama dalilin da ya sa Jamus ke ƙara mayar da hankali a kan yammacin Afirka. Jamus dai ta yi tayin ba da taimakon sojoji da za su horas da dakarun Afirka da za a tura arewacin Mali domin fatattakar masu kishin Islama.

Kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya ba wa ƙasashen Afirka wa'adin zuwa tsakiyar watan Nuwamba da su kammala shirye shiryen tura sojojin, kuma ko shakka babu shawarwarin kan girke sojoji na saman ajandar ziyarar ministan harkokin wajen na Jamus a Najeriya, inji Cornelius Vogt ƙungiyar nazarin manufofin ƙetare na Jamus.

"Haƙiƙa zai tattara ra'ayoyin shugabannin yankin sannan ya yi musu bayani dalla dalla game da buƙatun Jamus. Wato abin nufi girke sojojin zai samu nasara ne idan da ƙwaƙƙwaran shirin taimaka wa gwamnatin Mali."

Barazanar yaɗuwar aikin tarzoma

Außenminister Guido Westerwelle nach Ankuft in Dakar mit Senegals Verteidigungsminister Augustin Tine

Westerwelle da ministan tsaron Senegal Augustin Tine a birnin Dakar

Babban hatsarin da ake akwai shi ne idan arewacin Mali ka yia zama wani sansanin 'yan ta'adda da masu fataucin miyagun ƙwayoyi da garkuwa da mutane wanda hakan ka iya barazana ga Jamus da ma nahiyar Turai baki ɗaya. A ziyarar da ya kai Mali a tsakiyar wannan mako Westerwelle ya ce Jamus ka iya taka rawar mai shiga tsakani a rikicin ƙasar. Ya zuwa yanzu Jamus ba ta shiga a dama da ita a fagen siyasar yankin yammacin Afirka in ban da ɗaiɗaikun aikace aikace na tallafa wa tsarin demoƙarɗiyya. Sai dai a ra'ayin Kisma Gagou mashawarcin ma'aikatar tsaron Mali, yanzu lokaci yayi da za a samu sauyin manufa.

"Jamus za ta iya taka muhimmiyar rawa a yankin yammacin Afirka. Ba na ɗaukarta a matsayin tsohuwar 'yar mulkin mallaka. Ba ta gindaya tsauraran sharuɗɗa a taimakon raya ƙasa da take bayarwa."

Masana na fargabar cewa kai gwauro da mari da ministan harkokin wajen na Jamus ke yi a ƙasashen yammacin Afirka, ba zai ɗore ba, musamman idan aka dubi abubuwan da suka biyo bayan guguwar canjin da ta kaɗa a ƙasashen Larabawa da kuma alƙawuran da aka yi ta ɗauka bayan samun 'yancin Sudan ta Kudu.

Mawallafa: Peter Hille / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin