Manufofin Jamus a kasashen nahiyar Afirka | Siyasa | DW | 26.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Manufofin Jamus a kasashen nahiyar Afirka

A kokarin karfafa dangantaka da Afirka, ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi rangadin kwanaki hudu a wasu kasashen nahiyar Afirka guda uku.

A jawabin da ya yi ga manema labarai a yayin ziyarar ta sa ministan harkokin kasashen ketaren na Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nunar da cewa dole ne a bi a sannu wajen ganin an aiwatar da manufofin da Jamus din ke da su a nahiyar Afirka yadda ya kamata. Steinmeier ya kara da cewa in har ana son aiwatar da wasu manufofi sai an yi tunanin ta nutsu na inda ya kamata a dosa, sai dai ya ce kowa ya san abin da ya dace a yi. Ya kara da cewa akwai bukatar a mayar da hankali wajen aiwatar da dukkan manufofin da aka rubuta a kan takarda kan dangantakar Jamus da Afirka cikin tsanaki domin samun sakamako mai kyau wanda ya ce a kan shi ne suke ci gaba da aiki yanzu.

Karfafa huldar kasuwanci da gabashin Afirka

A yayin ziyarar ta sa dai ya fara ya da zango ne a kasar Habasha wato Ethiopia inda ya gana da mahukuntan kasar da kuma wakilan kungiyar Tarayyar Afirka kan karfafa dangantakar da ke tsakanin Jamus din da Afirka. Steinmeier ya kuma zarce kasar Tanzaniya inda ya kara jaddada aniyar Jamus ta kara yawan huldar kasuwancin da ke tsakaninsu yana mai cewa...

"Za mu yi amfani da danganatar kut-da-kut da ke tsakaninmu ta fuskar siyasa da kuma huldar kasuwanci da zuba jari har ma da shirin hadin gwiwa na bunkasa kasa da ke tsakaninmu da kudin shi ya kai sama da biliyan biyu na Euro. Muna son mu kara karfafawa da kuma inganta wannan dangantakar da ke tsakaninmu".

Ministan harkokin wajen na Jamus Frank-Walter Steinmeier ya kuma jaddada aniyar da Jamus din ke da ita na kara karfafa huldar kasuwanci da zuba jari da kuma taimako ga kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin gabashin Afirka wato EAC. Daga kasar ta Tanzaniya dai Steinmeier ya mika ne zuwa kasar Angola.

Bukatar kungiyoyin farar hula

Sai dai tun gabanin isarsa kungiyoyin farar hula suka fara bayyana bukatunsu da kuma bangaren da suke ganin ya kamata dangantakar Jamus din da Angolan ta fi mayar da hankali. Claudio Silva, shugaban wata kungiya da ke rajin kare 'yancin matasa a Angolan cewa yayi...

"Mun sha yin magana a kan cin hanci da karbar rashawa a Angola sai dai kuma matsalar ta cin hancin na da nasaba da wasu kasashen Turai da Amirka da ke yin yarjejeniyar da aka yi badakala a cikinta da ta shafi albarkatun kasar Angola wanda hakan ke ba da damar ci gaba da yin almundahana. Wannan ba wai matsala ce da take a Afirka kawai ba matsala ce da nahiyar Turai ma ke fuskanta. Ina son in san abun da Steinmeier zai yi wajen yakar cin hanci ba wai a Afirka kawai ba harma da kungiyar Tarayyar Turai".

Shi kuwa a nasa bangaren Rafael Morais na kungiyar da ke kare hakkin wadanda aka tasa domin gina hanyoyi ko kuma ma'aikatu a Angolan ya yi magana ne kan yadda kamfanonin kasashen ketare da ke Angolan ke take hakkin 'yan kasar.

"Abu na farko da muke bukata kamfanonin da ke zuba jari a Angola musamman ma na Jamus su mutunta hakkin dan Adam kasancewar shugabannin Angola ko kuma 'yan kasuwa na mayar da hankali ne kawai kan ribar da za su samu amma ba su damu da hakkin dan Adam ba, ya kamata su mutunta hakkin dan Adam a inda ake zubawa ko kuma za a zuba jari".

Dama dai a wani jawabi da ya yi a Tanzaniya Steinmeier ya jaddada bukatar kamfanonin kasashen ketare su rinka mutunta hakkin dan Adam a kasashen da suke zuba jari. Tuni dai Steinmeier ya isa kasar Angola da a yanzu haka tattalin arzikin ta ke bunkasa a nahiyar Afirkan tun bayan da aka gano albarkatun man fetur a kasar domin tataunawa kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da shugaban kasar Angolan Jose Eduardo dos Santos.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal