Maniyyata na samun matsaloli na izinin zuwa aikin Hajji | Siyasa | DW | 17.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Maniyyata na samun matsaloli na izinin zuwa aikin Hajji

Hukumomi a Filato sun sanar da cewar duk da wahalolin da ake samu tattare da samar wa maniyya izinin zuwa aikin Hajjin bana, za a yi jigilarsu tun daga ranar Alhamis.

Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Filato ta ce ta kammala shirin soma jigilar Alhazan jihar zuwa kasa mai tsarki somawa daga ranar Alhamis. To sai dai kuma akwai alamu cewar wasu da suka yi niyyar zuwa aikin Hajjin na bana ba za su sami damar sauke farali ba.

A bana dai akwai kimanin maniyyata daga jihar Filato su 1274, wadanda suka daura niyyar sauke farali. To amma kuma ga dukkan alamu wasu daga cikin maniyyatan aikin hajjin ba za su sami zarafin zuwa ba, don wasu dalilai da suka hada da jinkiri wajen neman bisa, ko kuwa rashin mika wa hukumar Alhazan takardar Form na zuwa aikin Hajji.

Ko da shi ke har lokacin da ake hada wannan rahoto hukumomin Alhazan na Filato suna kan kokarin tantance sunayen masu tafiya da kuma wadanda ba za su aikin Hajjin ba, don haka kenan akasarin maniyyata suna jira ne su ji an kira sunansu kafin su numfasa. To amma tun kafin zuwa wannan lokaci, wasu maniyyata da ba su amince a dauki muryoyinsu ba, sun cer muddin ba su sami tafiya ba, ba za su lamunta ba, ko da shi ke wasu cewa suka yi za su jira badi.

Flash-Galerie Pilgerfahrt (Hadsch) 2010

Dutsen Arafat: kololuwar aikin Hakki

A bara ma dai akwai maniyyata da dama da ba su sami zuwa ba don haka na zanta da wasu daga maniyyata na shekarar bara. Kasancewar har yanzu ba a kammala tantance sunayen ba, na tambayi sakataren hukumar Alhazan jihar Filato, Alhaji Salisu Musu, ko ina matsayin wadanda ba za su sami zuwa aikin Hajjin ba na bana?

Har zuwa maraicen Laraba babu wanda yake da yikinin zai sami zuwa, sai wanda yaji an kira sunansa, ko kuwa ya ga sunansa cikin jerin sunayen da aka fitar. Na tuntubi wasu da sunayensu ya fito kuma za su aikin Hajjin ko yaya suka ji.

Ana sa ran cewar tsakanin ranar Alhamis da Jumma'a za a kammala kwashe maniyyatan jihar Filato zuwa kasa mai tsarki, kasancewar na'ibin gwamnan jihar Filato Ingantius Lngjang, ya yi wa maniyatan jawabin ban kwana.

Sauti da bidiyo akan labarin