1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Mali

August 11, 2018

A zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Mali ana fafatawa ne tsakanin shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keïta da jagoran adawa Soumaïla Cissé, amma ana iya cewa 'yan adawa sun fadi zaben.

https://p.dw.com/p/330nY
Ibrahim Boubacar Keïta da Soumaïla Cissé
Ibrahim Boubacar Keïta da Soumaïla Cissé

Tun da fari dai 'yan takara 24 ne suka tsaya takara a zaben na kasar Mali sai dai 'yan takara biyu ne suka kai labarai. Duk da cewa 'yan takarar sun yi ta fatan samun nasara da ma sauya gwamnatin Ibrahim Boubacar Keïta da ake wa lakabi da IBK, sai dai kash, hakansu bai cimma ruwa ba, domin kuwa kwanaki kalilan gabanin zagaye na biyu na zaben na ranar 12 ga watan Agusta, sun rasa fata.

Aliou Diallo na daga cikin 'yan takarar da suka fafata a zagaye na farko na zaben kuma shi ne ma ya zo na uku da kaso takwas cikin 100 na kuri'un da aka kada. A yayin da ake sa ran zai goyi bayan dan takarar jam'iyyar adawa domin zuwa zagaye na biyu na zaben, sai ga shi ya bayyanawa magoya bayansa cewa za su yi kokarin lashe zabukan majalisun dokoki da gagarumin rinjaye domin su samu damar juya duk wanda aka rantsar a matsayin shugaban kasa a ranar hudu ga watan Satumbar wannan shekara, yana mai cewa:

Aliou Diallo: "Za mu mayar da hankali a kan zaben majalisar dokoki"
Aliou Diallo: "Za mu mayar da hankali a kan zaben majalisar dokoki"Hoto: DW/K. Gänsler

"Tilas mu samu kwarin gwiwa domin shirya wa zaben 'yan majalisun dokoki da ke tafe a watan Nuwamba mai zuwa. Tilas mu samu nasara wajen samun mafi rinjayen kujeru a majlisun ta yadda za mu iya juya duk shugaban kasar da ya samu darewa kan karagar mulki a ranar hudu ga watan Satumba mai zuwa."

Diallo da Cissé da kuma sauran 'yan takara 18 na daga cikin 'yan takara 24 da suka fafata a zagaye na farko na zaben kasar ta Mali. Duk da cewa masu sanya idanu a zaben zagayen farkon sun yaba da yadda ya gudana, 'yan takarar sun zargi gwamnati da tafka magudin zabe ta hanyar raba katinan zaben ba yadda ya kamata ba. Sai dai duk wannan sukan da 'yan adawar suka yi, bai hana hukumar zaben kasar bayyana sakamakon karshe na zaben a ranar Larabar da ta gabata ba, inda ta bayyana cewa IBK ya lashe zaben da kaso 41 da digo bakwai cikin 100 na kuri'un da aka kada.

'Yan Mali na fatan samun shugaban da zai cire musu kitse a wuta
'Yan Mali na fatan samun shugaban da zai cire musu kitse a wutaHoto: DW/K. Gänsler

Shin ko ya al'ummar Malin ke shirin yin zaben zagaye na biyu, kuma ko suna tunanin akwai wani sauyi da za a iya samu a kasar? Ga abin da wasu ke cewa:

"E a ganina zaben zai kawo sauyi mai tarin yawa a kasar nan, musamman idan muka samu shugaban kasar da ya cancanta wanda zai gyara mana kasarmu Mali."

Shi kuwa wannan cewa ya ke:

"Wannan ba wai wani tsari ne ko kuma aikin da 'yan takarar suka yi ne ya bai wa mutane sha'awa ba, da hakan ne kuwa da mun samu sakamakon da ya sha bamban."

Duk wanda zai lashe zaben, akwai jerin kalubale a gabanshi, musamman na rashin tsaro da ake fama da shi sakamakon ayyukan masu ikirarin Jihadi a arewacin kasar ta Mali.