Mali za ta samu tallafi daga kawayenta | Siyasa | DW | 29.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mali za ta samu tallafi daga kawayenta

kasashe da ke dasawa da Mali sun gudanar da taro a Addis Ababa inda suka yi alkawarin bayar da tallafin miliyan 340 na Euro domin gudanar da aiyukan soje da kuma na jin kai.

Ba a dai kai ga tantance tsabar kudi da kawayen Mali za su taimaka ma ta da su ba. Amma dai tuni Equatorial Guinea ta yi alkawari bayar da mai da ake bukata domin jigilar dakarun kasa da kasa. Yayin da su kuma sauran kasashen duniya suka ce za su gudanar da walau aiyukan jin kai ne ko kuma su bayar da tallafin kayan aiki. Da ma dai wadannan matsalolin ne, ummal aba'isan tafiyar hawainiya da aka fuskanta a yunkurin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO na afkawa masu kaifin kishin addinin Mali tun watannin da suka gabata. Ya zuwa yanzu dai dakarun kasashen Afirka guda 2000 ne suka isa Mali da kuma Nijar da ke makobtaka da ita, sakamakon karancin kudi da ya zame mata karfen kafa.

Yawan kudin da ake bukata a Mali

Malian soldiers wait at a checkpoint near Sevare on January 27, 2013. French-led troops were advancing on Mali's fabled desert city of Timbuktu on Sunday after capturing a string of other towns in their offensive against Islamist militant groups in the north of the country. Meanwhile, African leaders meeting in the Ethiopian capital were discussing scaling up the number of African troops to join the offensive, after the African Union's outgoing chief admitted the body had not done enough to help Mali. AFP PHOTO / FRED DUFOUR (Photo credit should read FRED DUFOUR/AFP/Getty Images)

Sojojin Mali ba su samu tallafi na Afirka ba

A lokacin bude taron na kawayen da ke dasawa da Mali, ECOWAS ko CEDEAO ta nunar da cewa ta na bukatar miliyon 960 na Dolar Amurka wajen cimma burin da ta sa a gaba. Sai dai kuma alkawarin da aka yi bai zarta rabin adadin wannan kaso ba. Kasashen Afirka sun nemi AU da ta kara yawan dakarunta a Mali matikar da ta na so a mayar da kasar tsintsiya madaurin ki daya. Burundi da kuma Tanzaniya sun ce a shirye suke su tura da sojojinsu zuwa Mali. Yayin da kasashen yammacin Afirka ta yamma za su kara kasonsu zuwa 5.400. A halin yanzu dai sojojin na Mali bisa rufin bayan takwarorinsu na Faransa ne ke fafatawa a filion daga. Sai dai Dr Mehari Tadele Maru, mai sharhi game da al'amuran da suka shafi siyasar kasa da kasa ya ce nahiyar Afirka ba za ta cire wa kanta kitse a wuta ba matikar ba ta samar da masu gida rana ba.

"Wannan ya na da nasaba da raunin da kungiyar Gamayyar Afirka da kuma ECOWAS ko CEDEAO suke fama da shi, a matsayinsu na wadanda ya kamata su magance wannan matsalar. Ba wai yunkuri na siyasa ne matsalar, amma kuma karanci kudi ne babban kalubalen da ake fama da shi."

Taimakon kasashen Afirka ga Mali

Mali Regierungstruppen auf dem Weg zu Hombori Bevölkerung

'Yan Mali na ci gaba da jinjina wa Faransa

Miliyon 350 ake bukata domin horas da sojojin Mali sabbin dabarun yaki. Ya zuwa yanzu ECOWAS So CEDAO ta ce tallafinta ba zai fi miliyon 10 na Dollar Amurka ba. Yayin da a karon farko cikin tarihi Kungiyar Gamayyar Afirka za ta bayar da miliyon 50 na Dollar. Ita ma dai Majalisar Dinkin Duniya ba ta kai ga bayar ga kason da za ta bayar domin kula da sojojin kasa da kasa da ke fafatwa a Mali ba. Sai kantoman Au da ke kula da harkokin zaman lafiya da tsaro Ramtan Lamamra ya nuna gamsuwa da yawan kudi da kasashen duniya suka yi alkawari, ya na mai cewa za su taimaka wajen daukar dawainiyar sojojin kasa da kasa na dan wani lokaci. Sai dai Salomon Ayele Derso na cibiyar nazarin al'amuran tsaro a Afirka, ya ce ba nan gizo ke saka ba.

"Lokacin da aka tafka muhawara a taron, an jadadda bukatar turawa da sojoji cikin hanzari a yankin da ake fama da rikici. Sai idan Kungiyar Gamayyar Afirka ta sauke wannan nauyi ne, za ta iya tinkarar duk wasu rikice rikice da za su kunno kai makamcin wanda ya ke gudana yanzu haka a Mali."

Shugaban Mali mai rikon kwarya Dioncounda Traore ya yi wa kawayen kasarsa godiya game da tallafi da su bayar wajen mayar ma ta da martaba. Hakazalika ya yi fatan ganin an gudanar da sahihin zabe a Mali kan nan da ranar 31 ga watan Julin 2013.

Rahoto cikin sauti na kasa

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin