1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: 'Yan bindiga sun kashe mutane a Mopti

August 20, 2023

Rahotanni daga Mali na nuni da cewa, 'yan bindiga sun kai hari a tsakiyar yankin Mopti mai fama da matsalar tsaro. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 21.

https://p.dw.com/p/4VMgt
Hoto: Sebastien Rieussec/Hans Lucas/IMAGO

Wata majiya ta ruwaito cewa, 'yan bindigar sun bude wuta ne ga al'ummar kauyen Yarou, inda wasu mutane 20 zuwa 30 suka jikkata. Har kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin. Mali da ke yankin yammacin Afirka na fama da matsalolin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai da ke da alaka da al-Qaeda da kuma IS, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane yayin da wasu miliyoyin suka rasa matsuganansu.