1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin ceto yarjejeniyar zaman lafiya

Ramatu Garba Baba
July 10, 2019

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya sanya sunayen wasu mutum 5 cikin jerin sunayen bara gurbi tare da takunkumin zirga-zirga bisa zargin yi wa shirin samar da zaman lafiya zagon kasa.

https://p.dw.com/p/3Lphi
Symbolbild - Tuareg in Mali
Hoto: picture-alliance/AP Photo//Rebecca Blackwell

Cikin mutanen biyar, har da wani Mohamed Ould Mataly dan majalisar kuma na jam'iyyar shugaba mai ci,  Ibrahim Boubacar Keita da kuma wani fitaccen dan kasuwa da aka zarga da laifuka na safarar miyagun kwayoyi. Wannan shi ne karo na biyu da kwamitin ke daukar irin wannan mataki a kasa da shekara guda, don ko a Disambar bara, an sanya sunayen wasu fitattun mutane uku cikin wannan kundi bisa zarginsu da aka yi da tallafawa ayyukan 'yan bindiga.

Mali ta dade tana fama da rikici a sanadiyar ayyukan kungiyoyi na masu kishin Islama da ke rike da wasu yankunan kasar, yunkurin shiga tsakani da majalisar dinkin duniya da kuma Faransa ke yi, ya ci tura inda maimakon shawo kan matsalar, rikicin kasar ke kara yaduwa zuwa kasashen da ke makwabtaka da Malin.